Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Yaya Zan Gane Addini na Gaskiya?

Ta Yaya Zan Gane Addini na Gaskiya?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda za mu iya sanin mabiyan addinin karya da mabiyan addinin gaskiya. Ya ce: ‘Za ku gane su ta irin aikinsu. Za a iya ciran inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya?’ (Matta 7:16, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda muke iya sanin bambancin da ke tsakanin itacen kaya da itacen inabi ta wajen ’ya’yansu, haka nan kuma za ka iya bambanta masu bin addini na gaskiya daga na karya ta wajen ayyukansu.

  1.   Mabiyan addini na gaskiya suna koyar da ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada ba ra’ayoyin ’yan Adam ba. (Yohanna 4:24; 17:17) Wannan koyarwar gaskiya ta hada da koyarwa game da kurwa da kuma rai na har abada a aljanna a duniya. (Zabura 37:29; Ishaya 35:5, 6; Ezekiyel 18:4) Kari ga hakan, suna fallasa koyarwar addinan karya.—Matta 15:9; 23:27, 28.

  2.   Addinin gaskiya yana taimaka wa mutane su san gaskiya game da Allah da kuma sunansa, Jehobah. (Zabura 83:18; Ishaya 42:8; Yohanna 17:3, 6) Ba ya sa mutane ganin kamar ba za a iya sanin halin Allah ba amma yana koya musu cewa Allah yana son mu kusace shi.—Yakub 4:8.

  3.   Addinin gaskiya yana koya wa mutane cewa ta wurin Yesu ne za a sami ceto. (Ayyukan Manzanni 4:10, 12) Kari ga haka, yana koya wa mabiyansa su bi umurnin Yesu da kuma misalinsa.—Yohanna 13:15; 15:14.

  4.   Addini na gaskiya yana koya wa mabiyansa su dogara da Mulkin Allah domin shi ne zai kawar da matsalolin ’yan Adam. Yana kuma sa mabiyansa su koya wa mutane game da wannan Mulkin.—Matta 10:7; 24:14.

  5.   Addinin gaskiya yana koya wa mutane su yi kaunar juna daga zuciya. (Yohanna 13:35) Yana koya wa mutane yadda za su daraja kowa ba tare da nuna wariya ba. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Mabiyansa ba sa zuwa yaki domin suna kaunar mutane.—Mikah 4:3; 1 Yohanna 3:11, 12.

  6.   Mabiyan addinin gaskiya ba su da limamai da suke biya kuma ba sa kiran juna da wasu lakabi na ban girma.—Matta 23:8-12; 1 Bitrus 5:2, 3.

  7.   Mabiyan addinin gaskiya ba sa saka hannu a siyasa. (Yohanna 17:16; 18:36) Amma suna yin biyayya ga gwamnati kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar [wato gwamnati], Allah kuma abin da ke na Allah.”—Markus 12:17; Romawa 13:1, 2.

  8.   Addinin gaskiya yana gyara rayuwar mutane domin mabiyansa suna bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki a kowane fannin rayuwarsu. (Afisawa 5:3-5; 1 Yohanna 3:18) Suna yi wa Allah ibada da farin ciki maimakon su yi kamar ana tilasta musu ne.—1 Timotawus 1:11, New World Translation.

  9.   Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mabiyan addinin gaskiya ba za su fi sauran mutane yawa ba. (Matta 7:13, 14) Ana wulakanta mabiyan addinin gaskiya kuma ana tsananta musu domin suna yin nufin Allah.—Matta 5:10-12.

Mutum ba zai iya zaban ‘addini na gaskiya’ bisa ga ra’ayinsa kawai ba

 Idan muka zabi wani addini saboda son zuciya hakan yana da hadari sosai. Littafi Mai Tsarki ya annabta lokacin da mutane za su “tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu.” (2 Timotawus 4:3) Akasin hakan, Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu rika bin ‘addini mai-tsarki marar-bāci a gaban Allah Ubanmu,’ ko da ba mutane da yawa ne suka amince da addinin ba.—Yakub 1:27; Yohanna 15:18, 19.