Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce sam ba shi ba ne! Jehobah Allah bai ƙudurta mutane su sha wahala ba. Amma, ma’aurata na farko suka yi tawaye da sarautar Allah, sun zaɓi su kafa nasu mizanai nagari da kuma munana. Sun juya wa Allah baya kuma suka sha azabar yin haka. A yau muna shan azabar mummunar zaɓensu. Amma ba Allah ba ne tushen shan wahalar ’yan Adam. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kowa sa’anda ya jarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” (Yaƙub 1:13) Kowa yana iya shan wahala—har ma da waɗanda Allah ya amince da su.