Koma ka ga abin da ke ciki

Allah Yana da Suna Kuwa?

Allah Yana da Suna Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Dukan mutane suna da suna. Bai dace Allah shi ma ya sami suna ba? A dangantakar ’yan Adam samun suna da kuma yin amfani da suna yana da muhimmanci. Ya kamata dangantakarmu da Allah ya zama dabam ne?

 A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ce: ‘Domin su sani kai, wanda sunanka Jehobah ne.’ (Zabura 83:18) Ko da yake yana da laƙabi da yawa, kamar su “Allah Maɗaukaki,” “Ubangiji Mamallaki,” da kuma “Mahalicci,” ya daraja masu bauta masa ta wurin gaya musu cewa su kira shi da sunansa.—Farawa 17:1; Ayyukan Manzanni 4:24, NW; 1 Bitrus 4:19.

 Juyin Littafi Mai Tsarki da yawa suna ɗauke da sunan Allah a Fitowa 6:3. Ayar ta ce: “Na bayana ga Ibrahim, da Ishaƙu, da Yaƙub, Allah Alƙadiru, amma da sunana Yahweh ban sanu garesu ba.”

 A Hausance Jehobah ne sunan Allah da ake amfani da shi cikin ƙarnuka da yawa. Ko da yake ɗalibai da yawa sun fi son “Yahweh,” an fi yin amfani da Jehobah a kusan ko’ina. An rubuta sashe na farko na Littafi Mai Tsarki a harshen Ibrananci ne da ake karatunsa daga hannun dama zuwa hagu, ba a Turanci ba. A harshen, an rubuta sunan da baƙaƙe huɗu ne, יהוה. Waɗannan baƙaƙe huɗu na harshen Ibrananci—an jera su YHWH.