Sunan Allah Yesu Ne?

Sunan Allah Yesu Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Yesu ya ce “ni Ɗan Allah ne” ko “Ɗan Allah.” (Yohanna 10:36; 11:4) Yesu bai taɓa ce shi Maɗaukakin Allah ba ne.

 A cikin addu’a ga Allah, Yesu ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.”—Matta 6:9.

 Yesu ya bayyana sunan Allah sa’ad da ya ja aya daga cikin Nassi na dā ya ce: “Ku ji ya Isra’ila; [Jehobah, NW] Allahnmu, [Jehobah, NW] ɗaya ne.”—Markus 12:29; Kubawar Shari’a 6:4.