Amsar Littafi Mai Tsarki

Mala’iku halittu ne da suka fi ‘yan Adam iko da kuma girma. (2 Bitrus 2:11) Suna rayuwa ne a sama ko inda halittun ruhu suke zama, kuma wurin ya fi samaniya da duniya martaba. (1 Sarakuna 8:27; Yohanna 6:38) Saboda haka, ana kiransu ruhohi.1 Sarakuna 22:21.

Daga ina ne mala’iku suka fito?

Allah ya yi amfani da Yesu, wanda Littafi Mai Tsarki ya ce da shi “ɗan fari . . . gaban dukan halitta,” wajen halittar mala’iku. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda Allah ya yi amfani da Yesu wajen halitta, ya ce: “A cikin [Yesu] aka halicci dukan abu, cikin sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu ganuwa da abubuwa marasa ganuwa.” (Kolosiyawa 1:13-17) Mala’iku ba sa aure kuma ba sa haifan ‘ya’ya. (Markus 12:25) Maimakon haka, kowanne cikin wadannan “ ’ya’yan Allah” halittarsa ne aka yi.Ayuba 1:6.

An halicci mala’iku da dadewa kafin a halicci duniya. A lokacin da Allah ya halicci duniya, mala’iku sun “yi sowa [‘tā da murya,’ NW ] don farin ciki.”Ayuba 38:4-7.

Mala’iku guda nawa ne a sama?

Littafi Mai Tsarki bai ba da yawan mala’ikun da ke sama ba, amma ya nuna cewa mala’iku suna da dimbin yawa. Alal misali, manzo Yohanna ya ga miliyoyin mala’iku a cikin wahayin da aka saukar masa.Ru’ya ta Yohanna 5:11.

Shin, kowane mala’ika yana da nasa suna da kuma nasa halin ne?

Littafi Mai Tsarki ya ambata sunayen mala’iku guda biyu: wato Mika’ilu da Jibrailu. (Daniyel 12:1; Luka 1:26) * Wasu mala’iku sun yarda cewa suna da suna, amma ba su ambata sunan ba.Farawa 32:29; Alƙalawa 13:17, 18.

Kowane mala’ika yana da halinsa. Mala’iku suna iya magana da juna. (1 Korintiyawa 13:1) Suna da azanci kuma suna iya yabon Allah. (Luka 2:13, 14) Kari ga haka, suna da ‘yanci su zabi abu mai kyau da marar kyau, kamar yadda ya faru a lokacin da wasu mala’iku suka goyi bayan Shaidan sa’ad da ya yi wa Allah tawaye.Matta 25:41; 2 Bitrus 2:4.

Mala’iku suna da matsayi a tsakaninsu ne?

E. Mala’ikan da ya fi iko da kuma matsayi shi ne Mika’ilu, wato shugaban mala’iku. (Yahuda 9; Ru’ya ta Yohanna 12:7) Seraphim mala’iku ne masu matsayi sosai kuma suna tsaye kusa da kursiyin Jehobah. (Ishaya 6:2, 6) Cherubim ma suna da matsayi mai girma a cikin mala’iku kuma ana ba su ayyuka na musamman. Alal misali, Cherubim ne suka yi gadin Lambun Adnin sa’ad da aka kore Adamu da Hauwa’u.Farawa 3:23, 24.

Mala’iku suna taimaka wa mutane kuwa?

E. A yau Allah yana amfani da mala’ikunsa don ya taimaka wa bayinsa masu aminci.

  • Allah yana amfani da mala’iku wajen yi wa bayinsa ja-gora a wa’azin Mulkin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Bayin Allah da kuma mutanen da suke musu wa’azi suna amfana daga wannan ja-gorancin.Ayyukan Manzanni 8:26, 27.

  • Mala’iku suna kāre ikilisiyar Kirista don kar mugayen mutane su bata ta.Matta 13:49.

  • Mala’iku suna kāre bayin Allah masu aminci.Zabura 34:7; 91:10, 11; Ibraniyawa 1:7, 14.

  • Nan ba da dadewa ba, mala’iku za su hada hannu da Yesu don su kawo karshen mugunta a duniya.2 Tasalonikawa 1:6-8.

Kowane mutum yana da mala’ikan da musamman yake kāre shi ne?

Ko da yake mala’iku suna taimaka wa bayin Allah su kāre amincinsu, hakan ba ya nufin cewa Allah ya ba wa kowane Kirista mala’ikan da zai kāre shi. * (Matta 18:10) Mala’iku ba sa kāre bayin Allah daga dukan jarrabobi da kuma gwajin da suke fuskanta. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah zai yi wa bayinsa “hanyar tsira” sa’ad da suke fuskantar gwaji ta wurin ba su hikima da karfin jimrewa.1 Korintiyawa 10:12, 13; Yakub 1:2-5.

Ra’ayoyin da ba daidai ba game da mala’iku

Karya: Dukan mala’iku suna da aminci.

Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mugayen ruhohi ko kuma ‘mala’iku da suka yi zunubi.’ (Afisawa 6:12; 2 Bitrus 2:4) Wadannan mugayen mala’ikun su ne aljanu, kuma su ne suka goyi bayan Shaidan a lokacin da ya yi wa Allah tawaye.

Karya: Mala’iku ba za su taba mutuwa ba.

Gaskiya: Za a hallaka Shaidan Iblis da mugayen ruhohi.Yahuda 6.

Karya: Mutane suna juya su zama mala’iku bayan sun mutu.

Gaskiya: Mala’iku halittu ne da kansu, ba ‘yan Adam da suka mutu ba ne suke zama mala’iku. (Kolosiyawa 1:16) Mutanen da suka tashi daga mutuwa kuma suka je sama ba za su sake mutuwa ba. (1 Korintiyawa 15:53, 54) Matsayinsu zai fi na mala’iku.1 Korintiyawa 6:3.

Karya: An halicci mala’iku domin su rika yi wa ‘yan Adam hidima.

Gaskiya: Mala’iku suna bin umurnin Allah ne, ba na ‘yan Adam ba. (Zabura 103:20, 21) Yesu da kansa ma ya ce zai nemi taimako daga wurin Allah ne, ba daga wurin mala’iku ba.Matta 26:53.

Karya: Za mu iya yin addu’a ga mala’iku don su taimake mu.

Gaskiya: Yin addu’a ibada ne, kuma Jehobah ne kadai ya cancanci mu yi masa sujjada. (Ru’ya ta Yohanna 19:10) Ya kamata mu yi addu’a ga Allah ne kadai, kuma ta wurin Yesu.Yohanna 14:6.

^ sakin layi na 10 Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “Lucifer” a Ishaya 14:12, kuma wasu suna ganin kamar shi ne sunan mala’ikan da ya mai da kansa Shaidan Iblis. Amma asalin kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a matsayin Lucifer tana nufin “mai walkiya.” Abin da ake tattaunawa a wannan surar ya nuna cewa ba Shaidan ne ake magana a kansa ba, amma ana magana ne game da daular Babila, wadda Allah zai kaskantar da ita saboda girman kanta. (Ishaya 14:4, 13-20) An yi amfani da kalmar nan “mai walkiya” don a yi wa daular Babila ba’a bayan da aka hallaka ta.

^ sakin layi na 21 Wasu suna ganin kamar yadda aka ‘yantar da Bitrus daga kurkuku ya nuna cewa yana da wani mala’ika musamman wanda yake kāre shi. (Ayyukan Manzanni 12:6-16) Amma mai yiwuwa almajiran Yesu da suka yi magana game da “mala’ikan [Bitrus]” sun dauka cewa wani mala’ikan da yake wakiltar Bitrus ne ya zo, a maimakon Bitrus da kansa.