Shin, Yin Caca Zunubi Ne?

Shin, Yin Caca Zunubi Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai yi dogon bayani a kan batun caca ba, za mu iya ganewa daga nazarin ka’idodin Littafi Mai Tsarki cewa yin caca zunubi ne a gaban Allah.—Afisawa 5:17. a

  •   Kwadayi ne yake sa mutane su yi caca kuma Allah ba ya son mai kwadayi. (1 Korintiyawa 6:9, 10; Afisawa 5:3, 5) Masu caca suna sa rai za su yi kudi daga hasarar wasu, amma Littafi Mai Tsarki ya haramta yin kyashi.—Fitowa 20:17; Romawa 7:7; 13:9, 10.

  •   Yin caca, ko da da kudi kadan ne, yana iya sa mutum ya zama mai son kudi.​—1 Timotawus 6:9, 10.

  •   A yawancin lokuta, masu yin caca suna dogara ne ga camfi ko kuma sa’a. Amma hakan bautar gumaka ne a gaban Allah kuma Allah ba ya amincewa da ibadar wadanda suke da irin wannan halin.—Ishaya 65:11.

  •   Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu yi aiki da karfinmu don mu ciyar da kanmu, maimakon mu yi sha’awar mallakar abin wasu. (Mai-Wa’azi 2:24; Afisawa 4:28) Wadanda suke bin wannan shawarar Littafi Mai Tsarki suna ‘yin aiki’ domin su sami abinci.—2 Tasalonikawa 3:10, 12.

  •   Caca tana sa mutum ya kasance da halin gasa kuma Littafi Mai Tsarki ya haramta hakan.—Galatiyawa 5:26.

a A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata caca sau daya ne kawai dangane da abin da sojojin Romawa suka yi a kan rigar Yesu domin biya wa kansu muradi.—Matta 27:35; Yohanna 19:23, 24; Contemporary English Version; Good News Translation.