Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Shin Aljanu Suna Wanzuwa da Gaske?

Shin Aljanu Suna Wanzuwa da Gaske?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Hakika, suna wanzuwa. Aljanu “mala’iku” ne da suka yi zunubi kuma su ruhohi ne da suka ki yin biyayya ga Allah. (2 Bitrus 2:4) Shaidan ne mala’ika na farko da ya mai da kansa aljani kuma Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne “sarkin aljanu.”—Matta 12:24, 26.

Tawaye da aka yi a zamanin Nuhu

Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin tawaye da wasu mala’iku suka yi a zamanin Nuhu, wato kafin a yi rigyawa. Ya ce: “’Ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka dauko wa kansu mata dukan wadanda suka zaba.” (Farawa 6:2) Wadannan mugayen mala’ikun ba ‘su rike matsayinsu’ ba a sama, amma suka canja jikinsu suka zama kamar ’yan Adam domin su yi jima’i da mata.—Yahuda 6.

Sa’ad da aka soma rigyawa, sai mala’ikun da suka yi tawaye suka canja siffarsu don su koma sama. Amma, Allah ya kore su daga cikin iyalinsa. Jehobah ya hukunta su kuma daya daga cikin hukunci da aka yi musu shi ne, ba za su iya sake sanya jiki irin na ’yan Adam ba.—Afisawa 6:11, 12.