Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Shin an Ambaci Purgatory a Littafi Mai Tsarki?

Shin an Ambaci Purgatory a Littafi Mai Tsarki?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A’a. Babu kalmar nan “purgatory” a Littafi Mai Tsarki kuma Kalmar Allah ba ta koyar da cewa za a tsarkake kurwar wadanda suka mutu a purgatory ba. * Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da zunubi da mutuwa da kuma yadda hakan ya karyata koyarwar purgatory.

  • Bangaskiya ga hadayar fansar Yesu ce ke tsabtace mutum, ba wata rayuwa a purgatory ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “jinin Yesu Dansa [dan Allah] yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka” kuma ya kara da cewa ‘Yesu Kristi . . . ya kwance mu daga zunubanmu cikin jininsa.’ (1 Yohanna1:7; Ru’ya ta Yohanna 1:5) Yesu “ya ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” ​—Matta 20:28.

  • Matattu ba su san kome ba. “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Wanda ya mutu ba ya iya sani ko jin kome, don haka, wutar purgatory ba za ta iya tsarkake shi ba.

  • Allah ba ya horar da mutum don zunubin da ya yi kafin ya mutu. Littafi Mai Tsarki ya ce “hakkin zunubi mutuwa ne” ya kuma ce “wanda ya mutu ya kubuta daga zunubi.” (Romawa 6:7, 23) Mutuwa ce kadai sakamakon zunubin da mutum ya yi.

^ sakin layi na 3 Littafin nan Orpheus: A General History of Religions ya bayyana ma’anar purgatory cewa, “babu wani abu da ya goyi bayan wannan ra’ayin a Linjila.” Hakan nan ma littafin nan the New Catholic Encyclopedia ya ce: “A bincike na karshe da aka yi, an gano cewa koyarwar nan ta Katolika game da purgatory ba ta cikin Littafi Mai Tsarki, amma bisa ga al’ada take.”​—Bugu na Biyu, Littafi na 11, shafi na 825

^ sakin layi na 8 Duba littafin nan New Catholic Encyclopedia, Bugu na Biyu, Littafi na 11, shafi na 824.