Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Dabba Mai Kawuna Bakwai da Ke Littafin Ru’ya ta Yohanna Sura 13?

Mene ne Dabba Mai Kawuna Bakwai da Ke Littafin Ru’ya ta Yohanna Sura 13?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Dabba mai kawuna bakwai da aka yi maganarsa a Ru’ya ta Yohanna 13:1 tana wakiltar dukan tsarin siyasa na duniya.

  •   Tana da iko, da karfi da kuma gadon sarauta kuma hakan ya nuna cewa gwamnati ce.—Ru’ya ta Yohanna 13:2.

  •   Tana sarauta bisa “kowace kabila da al’umma da kowane harshe da iri,” saboda haka, ta fi gwamnatin wata kasa karfi.—Ru’ya ta Yohanna 13:7.

  •   Tana da dukan halaye na dabbobi hudu da aka kwatanta cikin annabcin Daniyel 7:​2-8, har da kamanin damisa da kafafun bear da bakin zaki da kuma kahoni goma. An nuna cewa dabbobi da aka ambata a annabcin Daniyel suna wakiltar sarakuna ko kuma mulkokin siyasa da suka yi mulki bi da bi a manyan dauloli. (Daniyel 7:​17, 23) Saboda haka, dabbar da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna sura 13 tana wakiltar kungiyoyin siyasa.

  •   Ta fito daga “cikin teku,” wato, daga cikin dimbin jama’a da sun rikice, wadanda sune tushen gwamnatin ’yan Adam.​—Ru’ya ta Yohanna 13:1; Ishaya 17:12, 13.

  •   Littafi mai Tsarki ya ce wannan lambar ko sunan dabbar, wato 666, ‘lambar mutum ne.’ (Ru’ya ta Yohanna 13:17, 18) Wannan furucin ya nuna cewa dabbar da ke cikin Ru’ya ta Yohanna sura 13 dan Adam ne, ba ruhu ko kuma aljani ba.

 Ko da yake al’ummai suna iya hada kai a kan wasu kalilan batutuwa, amma suna yin hakan ne don su kāre iko da suke da shi maimakon su mika kai ga Mulkin Allah. (Zabura 2:2) Za su kuma hada kai don su yi yaki da rundunar Allah wadda Yesu Kristi ne shugabansu a yakin Armageddon, amma za a halaka wadannan al’umman a wannan yakin.​—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 19:19, 20.

“Kahoni goma da kawuna bakwai”

 A cikin Littafi Mai Tsarki, wasu lambobi suna da ma’ana ta alama. Alal misali, ana amfani da goma da bakwai don a yi nuni ga abin da yake cikakke. Abin da zai taimaka mana mu fahimci ma’anar kahoni goma da kawuna bakwai na dabbar da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna sura 13 shi ne “gunkin dabbar” da aka ambata daga baya cikin littafin, wato wani dabba mai launi ja mai haske kuma yana da kawuna bakwai da kuma kahoni goma. (Ru’ya ta Yohanna 13:​1, 14, 15; 17:3) Littafi Mai Tsarki ya ce kawuna bakwai na wannan dabba mai launi ja yana nufin “sarakuna bakwai,” ko kuma mulkoki.​—Ru’ya ta Yohanna 17:​9, 10.

 Hakazalika, kawuna bakwai na dabba da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna suna wakiltar mulkoki bakwai: mulkokin da suka yi sarauta a duniya kuma sun zalunta bayin Allah, wato Masar, Assuriya, Babila, Midiya da Farisa, Hellas, Roma, da kuma Biritaniya da Amirka. Idan muka kammala cewa wadannan kahoni goma suna wakiltar duk kasashe masu mulki, babba ko karami, to kambi da ke bisa kowane kaho ya nuna cewa kowace kasa ta yi sarauta a lokaci daya da gwamnatin siyasa da ke sarauta.