Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Ya Yarda da Kisan Aure Ne?

Littafi Mai Tsarki Ya Yarda da Kisan Aure Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya yarda da kisan aure. Amma, Yesu ya ba da dalili ɗaya ne kawai da za a iya kashe aure, ya ce: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci [jima’i ba cikin gamin aure] ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.”—Matta 19:9.

Allah ya ƙi jinin kisan aure na wayo, kuma na ruɗu. Shi kansa zai hukunta waɗanda suka bar abokan aurensu don wata ’yar hujja, musamman ma da niyya su auri wani ko wata.—Malachi 2:13-16; Markus 10:9.