Koma ka ga abin da ke ciki

An Yarda da Auren Mace Fiye da Ɗaya?

An Yarda da Auren Mace Fiye da Ɗaya?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A dā, Allah ya yarda mutum ya auri mace fiye da ɗaya. (Farawa 4:19; 16:1-4; 29:18-29) Amma ba Allah ne ya kafa auren mace fiye da ɗaya ba. Ya ba wa Adamu mata ɗaya kawai.

Allah ya ba wa Yesu Kristi izinin ya sake kafa Mizaninsa na farko na auren mace ɗaya. (Yohanna 8:28) Sa’ad da aka tambaye shi game da aure, Yesu ya ce: “Shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su, har ya ce, Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne wa matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya?”—Matta 19:4, 5.

Daga baya, Allah ya hure wani almajirin Yesu ya rubuta: “Bari kowanne mutum shi kasance da matar kansa, kowacce mace kuma da mijin kanta.” (1 Korinthiyawa 7:2) Littafi Mai Tsarki kuma ya ce duk Kirista namiji mai aure cikin ikilisiya da ke da matsayi na musamman dole ne ya zama “mijin mace ɗaya.”—1 Timothawus 3:2, 12.