Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Mene ne Ruhu Mai Tsarki?

Mene ne Ruhu Mai Tsarki?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

Ruhu mai tsarki ikon Allah ne, wato ikon da yake amfani da shi wajen yin aiki. (Mikah 3:8; Luka 1:35) Allah yana aika ruhunsa mai tsarki ta wajen yin amfani da karfinsa wajen cika nufinsa a duk inda yake so.—Zabura 104:30; 139:7.

An dauko kalmar nan “ruhu” cikin Littafi Mai Tsarki daga kalmar Ibrananci da ake kira ruʹach da kuma kalmar Helenancin da ake kira pneuʹma. Sau da yawa, wadannan kalmomin suna nufin ikon da Allah yake amfani da shi wajen yin aiki ko kuma ruhu mai tsarki. (Farawa 1:2) Amma Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da ruhu mai tsarki a wasu hanyoyi dabam-dabam:

  • Numfashi.—Habakkuk 2:19; Ru’ya ta Yohanna 13:15.

  • Iska.—Farawa 8:1; Yohanna 3:8.

  • Iko na musamman da ke sa halittu masu rai motsi.—Ayuba 34:14, 15.

  • Halin mutum.—Litafin Lissafi 14:24.

  • Ruhohi, kamar Allah da mala’iku.—1 Sarakuna 22:21; Yohanna 4:24.

Duka bayanan da muka yi a sama suna nuni ne ga wani abu da ’yan Adam ba sa gani da ido amma suna fahimtar aikin da yake yi da karfin da yake da shi. Hakazalika, ba a ganin ruhu mai tsarki na Allah domin yana nan kamar yadda ba a ganin “iska amma yana da karfi sosai.”—An Expository Dictionary of New Testament Words, by W.  E. Vine.

Littafi Mai Tsarki ya sake yin nuni ga ruhu mai tsarki na Allah a matsayin “hannuwansa” da kuma ‘yatsotsinsa.’ (Zabura 8:3; 19:1; Luka 11:20; gwada Matta 12:28) Kamar yadda mai sana’a yakan yi amfani da hannuwansa da yatsosinsa ya yi aikinsa, hakan nan ma Allah ya yi amfani da ruhunsa ya yi wadannan abubuwa:

  • Sararin samaniya.—Zabura 33:6; Ishaya 66:1, 2.

  • Littafi Mai Tsarki.—2 Bitrus 1:20, 21.

  • Mu’ujizai da bayinsa na dā suka yi da kuma kwazon da suka yi a yin wa’azi.—Luka 4:18; Ayyukan Manzanni 1:8; 1 Korintiyawa 12:4-11.

  • Halaye na kirki da wadanda suke masa biyayya suke nunawa.—Galatiyawa 5:22, 23.

Ruhu mai tsarki ba mutum ba ne

Littafi Mai Tsarki ya ambata ruhu mai tsarki na Allah a matsayin “hannuwansa” da ‘yatsotsinsa’ ko kuma “numfashinsa.” Hakan ya nuna cewa ruhu mai tsarki ba mutum ba ne. (Fitowa 15:8, 10) Hannuwan mai sana’a ba ya aiki ba tare da zuciyarsa ko kuma jikinsa ba. Hakazalika, Allah ne ke sa ruhunsa ya yi kamar yadda yake so. (Luka 11:13) Littafi Mai Tsarki ya sake kwatanta ruhun Allah da ruwa kuma ya kamanta shi da bangaskiya da kuma ilimi. Duk wadannan kwatancin suna tabbatar da cewa ruhu mai tsarki ba mutum ba ne.Ishaya 44:3; Ayyukan Manzanni 6:5; 2 Korintiyawa 6:6.

Littafi Mai Tsarki ya ambata sunan Jehobah Allah da kuma Dansa, Yesu Kristi; amma babu wani wuri da aka ambaci sunan ruhu mai tsarki. (Ishaya 42:8; Luka 1:31) Sa’ad Istifanus wanda aka kashe don imaninsa ya ga wahayi na samaniya, ya ga mutane biyu ne kawai amma ba uku ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shi, cike da Ruhu Mai-tsarki, ya zuba ido zuwa sama, ya ga darajar Allah, da Yesu a tsaye ga hannun dama na Allah.” (Ayyukan Manzanni 7:55) Ruhu mai tsarki da aka ambata iko ne da Allah ya yi amfani da shi ya sa Istifanus ya ga wahayin nan.

Ra’ayoyi da ba su dace ba game ruhu mai tsarki

Ra’ayin karya: Juyin King James version ya fassara littafin 1 Yohanna 5:7, 8 cewa ruhu mai tsarki mutum ne kuma shi daya ne cikin Allah-uku-cikin daya.

Gaskiya: Juyin King James na Littafi Mai Tsarki ya dada kalaman nan a 1 Yohanna 5:7, 8 cewa: “a sama, Uba da Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki: Su ukun sun zama daya. Kuma akwai guda uku da suke ba da shaida a duniya.” Amma masu bincike sun gano cewa manzo Yohanna bai rubuta wadannan kalaman ba, saboda haka, ba sa cikin asalin rubutun Littafi Mai Tsarki. Farfesa Bruce M. Metzger ya ce: “Babu shakka, wadannan kalaman ba gaskiya ba ne kuma bai kamata suna cikin littattafan Sabon Alkawari ba.”A Textual Commentary on the Greek New Testament.

Ra’ayin karya: Littafi Mai Tsarki ya kamanta ruhu mai tsarki da mutum, hakan ya nuna cewa ruhu mai tsarki mutum ne.

Gaskiya: A wasu lokuta, Nassosi sun kwatanta ruhu mai tsarki da mutum, amma hakan ba ya nufin cewa ruhu mai tsarki mutum ne ba. Littafi Mai Tsarki ya kuma kwatanta hikima, mutuwa, zunubi da mutane. (Misalai 1:20; Romawa 5:17, 21) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce hikima tana da ‘ayyuka’ da kuma ‘’ya’ya.’ Ya kuma kwatanta zunubi cewa yana iya yaudara, yana iya kashe mutum kuma yana mugun kishi.—Matta 11:19; Luka 7:35; Romawa 7:8, 11.

Hakazalika, sa’ad da manzo Yohanna yake kaulin abin da Yesu ya ce, ya ambata ruhu mai tsarki a matsayin “mataimaki” wanda zai ba da tabbaci da ja-gora kuma ya yi magana, ya yi shela, ya daukaka, kuma ya karba. Ya yi amfani da wakilin suna na namiji, wato “shi” a lokacin da yake ambata wannan “mataimakin.” (Yohanna 16:7-15) Ya ambaci hakan ne domin kalmar nan (pa·raʹkle·tos) wato “mataimaki” a Helenanci namiji ne kuma cikin jituwa da ka’idodin Helenanci, ya dace a hada shi da wakilin sunan namiji. Lokacin da Yohanna ya ambaci ruhu mai tsarki, ya ambace shi ne da na nuna cewa ba namiji ko tamace ba ne.—Yohanna 14:16, 17.

Ra’ayin karya: Baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki ya nuna cewa ruhu mai tsarki mutum ne.

Gaskiya: A wasu lokuttan, “suna” a cikin Littafi Mai Tsarki na wakiltar karfi ko iko. (Kubawar Shari’a 18:5, 19-22; Esther 8:10) Hakan ya yi daidai da wani kalami da ake yi a harshen Turanci, wato “a cikin sunan doka.” Hakan ba ya nufin cewa dokar mutum ne. Idan aka yi wa mutum baftisma “cikin sunan” ruhu mai tsarki, hakan ya nuna cewa mutumin ya fahimci matsayin ruhu mai tsarki da kuma yadda Allah yake yin amfani da shi don cika nufinsa.—Matta 28:19.

Ra’ayin karya: Manzannin Yesu da wasu almajirai na farko sun yi imani cewa ruhu mai tsarki mutum ne.

Gaskiya: Littafi Mai Tsarki bai fadi haka ba, kuma tarihi ma bai nuna haka ba. Littafin Encyclopædia Britannica ya ce: “An samo tushen ra’ayin cewa Ruhu Mai Tsarki wani abu ne mai Rai . . . daga Majalisar ’yan Constantinople a shekara ta 381.” Hakan ya faru ne shekaru sama da 250 bayan mutuwar manzo na karshe.