Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Mulkin Allah?

Mene Ne Mulkin Allah?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Mulkin Allah gwamnati ce ta ainihi da Jehobah Allah ya kafa. A cikin Littafi Mai Tsarki ana ce da “mulkin Allah,” “mulkin sama” domin yana sarauta daga sama. (Markus 1:14, 15; Matta 4:17) Gwamnati ce irin ta mutane, duk da haka ta fi ta mutane a kowane fasali.

  •   Masarauta. Allah ya naɗa Yesu Kristi Sarkin Mulkin kuma ya ba shi iko fiye da wani masarauci ɗan Adam da ake da shi. (Matta 28:18) Yesu yana amfani da wannan ikon a yin nagarta ne kawai, tun da yake ya nuna cewa shi Shugaba ne wanda za a iya dogara gareshi kuma mai juyayi. (Matta 4:23; Markus 1:40, 41; 6:31-34; Luka 7:11-17) Tare da jagorar Allah, Yesu ya zaɓi mutane daga dukan al’ummai da za su yi “mulki bisa duniya” da shi a sama.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.

  •   Tsawon Lokacin. Mulkin Allah za ya “tsaya har abada,” ba kamar gwamnatoci na ’yan Adam da yau suna nan goɓe ba su ba.—Daniel 2:44.

  •   Talakawan. Duk wanda ya yi abin da Allah ke bukata gareshi zai iya zama talikin Mulkin Allah, ko daga ina ya fito.—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.

  •   Dokoki. Dokoki (ko kuwa umurnan) Mulkin Allah ba haramta munanan halaye ne kawai za su yi ba. Suna tsabtata ɗabi’ar talakawan. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka kuma ita ce ta fari. Ta biyu mai-kamaninta kuma ta ce, “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:37-39) Ƙaunar Allah da maƙwabci zai sa talakawan Mulkin su aikata da kyau yadda zai amfane wasu.

  •   Ilimi. Da yake Mulkin Allah zai kafa wa talakawansa mizanai, zai kuma koyar da mutane yadda za su bi mizanan.—Ishaya 48:17, 18.

  •   Aikin. Mulkin Allah ba zai wadata masu sarautan kuma ya cuci talakawansa ba. Maimakon haka, zai cika nufin Allah, har da alkawarinsa cewa waɗanda suke ƙaunarsa za su rayu har abada a duniya.—Ishaya 35:1, 5, 6; Matta 6:10; Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.