Amsar Littafi Mai Tsarki

A cikin Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da kalmar nan “sama” a hanyoyi uku: (1) sarari; (2) wurin da halittun ruhu suke da kuma (3) alamar matsayi mai girma. A duk lokacin da aka yi amfani da wannan kalmar, batun da ake tattaunawa ne zai taimake mu mu fahimci ainihin abin da ake nufi. *

 1. Sarari. Wannan yana nufin sararin sama inda iska ke hurawa, inda tsuntsaye suke yawo, inda ake yin hadari ko kankara da kuma inda ake ganin walkiya. (Zabura 78:26; Misalai 30:19; Ishaya 55:10; Luka 17:24) Yana kuma iya nufin inda “rana da wata da taurari” suke.—Kubawar Shari’a 4:19; Farawa 1:1.

 2. Wurin da halittun ruhu suke. “Sama” tana iya nufin wurin da halittun ruhu suke, wato, ba duniya ko sararin samaniya ba, kuma irin rayuwar da ke yi a wurin ya fi na duniya. (1 Sarakuna 8:27; Yohanna 6:38) Jehobah, wanda shi “Ruhu ne,” da kuma mala’iku ne suke zama a wannan wurin. (Yohanna 4:24; Matta 24:36) A wani lokaci ana iya amfani da kalmar nan “sammai” idan ana maganar mala’iku masu aminci wato, “taron halittu masu tsarki.”​—Zabura 89:5-7, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

  Kari ga hakan, Littafi Mai Tsarki yana amfani da kalmar nan “sama” idan yana nufin ‘mazaunin’ Jehobah. (1 Sarakuna 8:43, 49; Ibraniyawa 9:24; Ru’ya ta Yohanna 13:6) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a jefar da Shaidan da aljannunsa daga sama, wato, ba za a sake yarda musu su je gaban Jehobah ba. Amma za su ci gaba da zama halittun ruhu.—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9, 12.

 3. Alamar matsayi mai girma. A cikin Littafi Mai Tsarki akan yi amfani da kalmar nan “sama” idan ana maganar matsayi mai girma, musamman idan ana magana game da wadanda suke mulki. Wadanda za a iya kwatanta da wannan kalmar su ne:

  • Jehobah, wanda shi ne Madaukakin sama da kasa duka.​—2 Labarbaru 32:20; Luka 15:21.

  • Mulkin Allah, wato, gwamnatin da za ta sauya sarautar ’yan Adam. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan Mulkin “sababbin sammai.”—Ishaya 65:17; 66:22; 2 Bitrus 3:13. *

  • Kiristocin da suke da begen zuwa sama.​—Afisawa 2:6.

  • ’Yan Adam masu mulki da suka daukaka kansu bisa talakawansu.​—Ishaya 14:12-14; Daniyel 4:20-22; 2 Bitrus 3:7.

  • Aljannun da suke iko da duniya.​—Afisawa 6:12; 1 Yohanna 5:19.

Yaya sama take?

Halittun ruhu suna aiki tukuru. Miliyoyin halittun ruhu suna “aikata nufin” Jehobah.​—Zabura 103:20, 21, Juyi Mai Fitar da Ma’ana; Daniyel 7:10.

Littafi Mai Tsarki ya ce sama yana da haske sosai. (1 Timotawus 6:15, 16) Annabi Ezekiyel ya lura cewa sama tana da ‘haske’ sosai a cikin wahayin da aka nuna masa, amma a cikin wahayin da aka nuna wa Daniyel, Daniyel ya ga “kogin wuta.” (Ezekiyel 1:26-28; Daniyel 7:9, 10, Littafi Mai Tsarki) Sama wuri ne mai tsarki, da tsabta kuma yana da kyan gani sosai.​—Zabura 96:6; Ishaya 63:15; Ru’ya ta Yohanna 4:2, 3.

Yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta sama yana da ban sha’awa sosai. (Ezekiyel 43:2, 3) Duk da haka, ’yan Adam ba za su iya gane gaba daya yadda sama take ba domin bayanin ya fi karfinsu.

^ sakin layi na 3 Asalin kalmar Ibrananci da ake yin amfani da ita a matsayin “sama” tana nufin abin da ke da “tsawo” ko kuma abin da aka “daukaka.” (Misalai 25:3) Ka duba The New Brown, Driver, and Briggs Hebrew and English Lexicon of the Old Testament, shafi na 1029.

^ sakin layi na 9 McClintock and Strong’s Cyclopedia ya ce sabbabin sammai da aka ambata a Ishaya 65:17 yana nufin “sabuwar gwamnati da kuma sabon mulki.”​—Na IV, shafi na 122.