Amsar Littafi Mai Tsarki

Idan muka yi rashin wani, yana da sauki mu soma tunanin abin da ya sa mutane ke mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Karin mutuwa zunubi ne.”1 Korintiyawa 15:56.

Me ya sa dukan mutane suke zunubi kuma suke mutuwa?

Mutane na farko, Adamu da Hawwa’u sun mutu saboda sun yi zunubi ga Allah. (Farawa 3:17-19) Mutuwa ce kawai sakamakon tawayen da suka yi wa Allah, domin a gare shi ne “mabulbular rai ta ke.”Zabura 36:9; Farawa 2:17.

Dukan zuriyar Adamu sun sami illar zunubin da ya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum daya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Dukan mutane suna mutuwa domin sun yi zunubi.Romawa 3:23.

Yadda za a kawar da mutuwa

Allah ya yi alkawarin cewa zai “haɗiye mutuwa har abada.” (Ishaya 25:8) Kafin a kawar da mutuwa, dole ne a cire tushenta, wato zunubi. Allah zai yi wannan ta wurin Yesu Kristi, wanda ‘ya dauke zunubin duniya!’Yohanna 1:29; 1 Yohanna 1:7.