Koma ka ga abin da ke ciki

Iblis Zai Iya Mallakar ’Yan Adam Kuwa?

Iblis Zai Iya Mallakar ’Yan Adam Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Iblis da aljannu suna iko sosai bisa mutane shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka kuwa tana hannun Mugun.” (1 Yohanna 5:​19, Juyin New Century Version) Littafi Mai Tsarki ya ambata hanyoyin da Iblis ke iko a kan mutane.

  • Rudu. Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu “dage gāba da kissoshin Iblis.” (Afisawa 6:​11) Wata yaudarar da yake amfani da shi na rudin mutane shi ne cewa mabiyan iblis wai sune ainihin bayin Allah.​—2 Korintiyawa 11:13-​15.

  • Sihiri. Iblis yana yaudarar mutane ta wurin sihiri, masu duba, da masu duban masanan taurari. (Kubawar Shari’a 18:10-​12) Shan kwaya, dabarcewa, da kuma rashin tunanin kirki yana ba wa aljannu zarafin su yi iko da mutum.​—Luka 11:24-​26.

  • Addinin Karya. Addinai da suke koyar da karya suna yaudarar mutane su ki biyayya ga Allah. (1 Korintiyawa 10:20) Littafi Mai Tsarki ya ce irin imanin “koyarwar aljannu” ne.​—1 Timotawus 4:1.

  • Mallaka. Littafi Mai Tsarki yana dauke da labarin mutane da aljannu suka mallake su. Wani lokaci ma mutanen da aljannu suka mallake su sukan makanta, ko su zama bebaye har ma su raunar da kansu.​—Matta 12:22; Markus 5:​2-5.

Yadda za mu guje wa ikon Iblis

Ba ka bukatar ka shaku da tsoron mallaka na aljannu ba, domin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za ka iya tsayayya wa Iblis:

  • Ka koya ka san dabarar Iblis domin kada ka yi “rashin sanin makidansa.”​—2 Korintiyawa 2:​11.

  • Ka koyi Littafi Mai Tsarki kuma ka yi amfani da abin da kake koyo. Idan kana amfani da ka’idodin Littafi Mai Tsarki zai tsare ka daga ikon Iblis.​—Afisawa 6:​11-​18.

  • Ka wasar da dukan abin da yake na aljannu. (Ayyukan Manzanni 19:19) Hakan ya hada da waka, littattafai, mujallu, kasidai da bidiyoyinsu.