Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Mene ne “Mabudan Mulkin”?

Mene ne “Mabudan Mulkin”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A wasu lokuta ana iya kiran ‘mabudan Mulki’ “mabudan zuwa Mulkin,” kuma hakan yana wakiltar ikon bude wa mutane kofar “shiga Mulkin Allah.” (Matta 16:19; Littafi Mai Tsarki; Ayyukan Manzanni 14:22) * Yesu ne ya ba wa Bitrus “mabuɗan Mulkin sama.” Hakan ya nuna cewa an ba wa Bitrus ikon bayyana yadda amintattun bayin Allah da suka sami ruhu mai tsarki za su more gatan shiga Mulkin Allah.

Su waye ne suka amfana daga mabudan?

Ga rukuni uku da Bitrus ya yi amfani da wannan ikon don ya taimaka musu su sami gatan shiga Mulkin Allah:

  1. Yahudawa da Yahudawa da suka juya/⁠ Wadanda suka zama Yahudawa. Jim kadan bayan mutuwan Yesu, Bitrus ya karfafa wasu mabiya addinin Yahudawa su ba da gaskiya ga Yesu cewa, shi Allah ya zaba don ya yi sarauta a Mulkin. Bitrus ya bayyana musu abin da za su yi idan suna so su sami ceto. Abin da ya gaya musu ya sa su sun san yadda za su shiga Mulkin Allah, kuma mutane da yawa sun amince da “Magana tasa.”​​—⁠Ayyukan Manzanni 2:​38-41.

  2. Samariyawa. Daga baya, an aike Bitrus zuwa wurin Samariyawa. * A wannan karon, ya sake amfani da mubudin Mulkin kuma da shi da manzo Yohanna, “suka yi masu addu’a” don su sami ruhu mai tsarki. (Ayyukan Manzanni 8:​14-17) Hakan ya ba wa Samariyawa damar shiga Mulkin sama.

  3. ‘Yan Al’ummai. Shekara uku da rabi bayan Yesu ya mutu, Allah ya nuna wa Bitrus a wahayi cewa ‘Yan Al’ummai (wato wadanda ba Yahudawa ba) za su sami damar shiga Mulkin Allah. A nan ma, Bitrus ya yi amfani da daya daga cikin mabudin don ya yi wa ‘Yan Al’ummai wa’azi, kuma hakan ya sa sun sami ruhu mai tsarki, suka zama Kiristoci, sa’an nan suka sami gatan zama wadanda za su yi sarauta a Mulkin Allah.​ ​—⁠Ayyukan Manzanni 10:​30-35, 44, 45.

Mene ne “shiga Mulkin” yake nufi?

Wadanda suka sami “shiga Mulkin” za su yi mulki tare da Yesu a sama. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za su “zauna bisa kursiyai” kuma su zama sarakunan da za su yi “mulki bisa duniya.”​​—⁠Luka 22:​29, 30; Ru’ya ta Yohanna 5:​9, 10.

Ra’ayin da ba daidai ba game mabudan Mulki

Karya: Bitrus ne yake zaban wadanda za su je sama.

Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ne yake, “shar’anta masu-rai da matattu” ba Bitrus ba. (2 Timotawus 4:​1, 8; Yohanna 5:22) Kari ga haka, Bitrus ma da kansa ya ce Yesu ne “Allah ya sanya shi Mai-shari’a na masu-rai da matattu.”​—⁠Ayyukan Manzanni 10:​34, 42.

Karya: Ana jiran Bitrus a sama ya yanke hukuncin lokacin da za a yi amfani da mabudan Mulkin.

Gaskiya: Bayan da Yesu ya yi wa Bitrus magana game da mabudan Mulkin, sai ya ce: “Dukan iyakar abin da ka ɗaure a duniya a ɗaure za ya zama a sama: kuma dukan abin da ka kwance a duniya a kwance za ya zama a sama.” (Matta 16:19) Wasu mutane suna ganin kamar abin da wurin nan yake nufi shi ne, Bitrus ne yake yanke shawara a sama. Amma asalin abin da aka rubuta a wurin da Helenanci ya nuna cewa, Bitrus ne yake bin duk wani shawarar da aka yanke a sama ba shi ne yake fadan abin da za a yi a sama ba. *

Akwai wani wuri a Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa, ko da yake Bitrus ne ke rike da mabudan Mulki, yana bin umurnin da aka ba shi daga sama. Alal misali, ya bi umurnin da Allah game da yadda zai yi amfani da mubudi na uku da aka ba shi.​​—⁠Ayyukan Manzanni 10:​19, 20.

^ sakin layi na 3 A wasu lokuta Littafi Mai Tsarki yana amfani da kalmar nan “mabudi” a matsayin iko ko kuma gata.​​—⁠ Ishaya 22:​20-22; Ru’ya ta Yohanna 3:​7, 8.

^ sakin layi na 7 Addinin da Samariyawa suke bi dabam ne da na Yahudawa amma suna amfani da wasu daga cikin dokar da Allah ya ba Musa.

^ sakin layi na 15 Ka duba almar nazari da ke Matta 16:19 na New World Translation of the Holy Scriptures (Study Edition).