Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Zanen Jiki?

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Zanen Jiki?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

Sau daya ne kawai aka ambata zanen jiki, wato tattoo a cikin Littafi Mai Tsarki. Levitikus 19:28 ya ce: “Ba kuwa za ku yi shasshawa [zane] a fatarku ba.” Ga al’ummar Isra’ila ce Allah ya ba da umurnin nan domin a bambanta su daga sauran al’umman da ke tsatsage fatarsu ta wajen rubuta sunaye ko kuma alamun allolinsu. (Kubawar Shari’a 14:2) Ko da yake Kiristoci ba sa karkashin dokar da aka ba Isra’ilawa, amma ka’idarsa ta shafe su kwarai da gaske.

Shin ya kamata Kirista ya yi zanen jiki?

Ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke biye za su taimake ka ka yi tunani sosai a kan wannan batun:

  • “Mata kuma su riƙa sa tufafin da ya dace da su saboda kunya.” (1 Timotawus 2:9, Littafi Mai Tsarki) Wannan ka’idar ta shafi mata da maza. Ya kamata mu yi la’akari da yadda wasu su ke ji kuma kada ya zama muna jawo hankalin mutane ne a kanmu saboda irin adon da muke yi.

  • Wasu suna zanen jiki domin su nuna yancin kansu, wasu kuma suna yin haka ne don su nuna cewa sune suke da iko bisa jikinsu. Amma, Littafi Mai Tsarki ya karfafa Kiristoci cewa: “Ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.” (Romawa 12:1, Littafi Mai Tsarki) Ya kamata ka yi tunani, yin zanen jiki zai iya shafan ‘ibadata ta ainihi’ ga Allah kuwa? Idan kana zanen jiki domin yayinsa ake yi ko kuma don kana so ka nuna irin abokan da kake bi, ka tuna cewa za ka iya canza ra’ayinka amma ba za ka iya share zanen da ka yi a jikinka ba. Idan ka yi tunani sosai game da abin da ya sa kake so ka yi zanen, hakan zai taimake ka wajen yanke shawara mai kyau.—Misalai 4:7.

  • “Tunanin mai-himma zuwa yalwata kadai su ke nufa: Amma kowane mai-garaje wajen tsiya ya ke nufa.” (Misalai 21:5) A yawancin lokuta mutane suna yin zanen jiki ba tare da neman shawara ba, kuma hakan yakan shafi dangantakar mutumin da wasu kuma ya hana shi samun aikin albashi. Yin zanen jiki yana da tsada kuma share shi bai da sauki kuma da zafi. Bincike da aka yi da kuma masu sana’ar share zanen jiki sun tabbatar da cewa yawancin wadanda suke dauke da wannan zanen sun yi da-na-sani daga baya.