Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Lamba Take Nufi a Cikin Littafi Mai Tsarki? Hisabi Bisa Littafi Mai Tsarki Ne?

Mene Ne Lamba Take Nufi a Cikin Littafi Mai Tsarki? Hisabi Bisa Littafi Mai Tsarki Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A yawancin lokaci Littafi Mai Tsarki yana amfani da lamba a zahiri, amma a wani lokacin ana amfani da shi a alamance. Mahallin yakan nuna yadda aka yi amfani da lamba ko a alamance ne. Yi la’akari da wadannan misalan ma’anar lambobi da suke a alamance da aka yi cikin Littafi Mai Tsarki:

  •   1 Hadin kai. Alal misali, Yesu ya yi addu’a ga Allah cewa mabiyansa “su zama daya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka.”—Yohanna 17:20, 21; Matta 19:6.

  •   2 A batun shari’a, shaidu biyu ne suke tabbatar da maganar. (Kubawar Shari’a 17:6) Hakazalika, maimaitawar wahayi ko kuma batu yana nuna cewa al’amarin gaskiya ce. Alal misali, sa’ad da Yusufu ya bayyana ma’anar mafarkin Fir’auna sarkin Masar, ya ce: “Saboda wannan aka maimaita mafarkin so biyu ga Fir’auna, domin a wurin Allah matsalan ta tabbata, yanzu kuwa Allah za ya faradda shi.” (Farawa 41:32) Game da annabce, “kaho biyu” ya wakilta sarakuna biyu, kamar yadda aka gaya wa annabi Daniyel game da Daular Media da Persia.—Daniyel 8:20, 21; Ru’ya ta Yohanna 13:11.

  •   3 Kamar yadda shaidu uku suke tabbatar da cewa al’amarin gaskiya ce, idan aka maimaita abubuwa sau uku suna nuna cewa al’amarin gaskiya ce.—Ezekiel 21:27; Ayyukan Manzanni 10:9-16; Ru’ya ta Yohanna 4:8; 8:13.

  •   4 Hakan zai iya wakilta wani abin da ya cika nufinsa. Alal misali, “iskoki hudu na duniya” da ke nufin ikon halaka da ya fito daga dukan fadin duniya.—Ru’ya ta Yohanna 7:1; 21:16; Ishaya 11:12.

  •   6 Bakwai sauran daya, da a yawancin lokaci yake wakiltar abin da ke cikakke, shida kuma yana wakiltar wani abin da bai cika ba ko ajizi ko kuma wani abin da ke wakiltar magabtan Allah.—1 Labarbaru 20:6; Daniyel 3:1; Ru’ya ta Yohanna 13:18.

  •   7 A yawancin lokaci wannan lambar tana wakiltar abin da ke cikakke. Alal misali, Allah ya umurci isra’ilawa su zaga birnin Yariko na kwanaki bakwai kuma su kewaye ta so bakwai a rana ta bakwan. (Joshua 6:15) Littafi Mai Tsarki yana dauke da misalai da yawa game da yadda aka yi amfani da lambar nan bakwai. (Levitikus 4:6; 25:8; 26:18; Zabura 119:164; Ru’ya ta Yohanna 1:20; 13:1; 17:10) Sa’ad da Yesu ya ce wa Bitrus ya gafarta wa dan’uwansa ba “har so bakwai ba; amma, Har bakwai bakwai so saba’in,” yadda ya maimaita “bakwai” yana nufin “ba iyaka.”—Matta 18:21, 22.

  •   10 Wannan lambar tana iya nufin abu gaba daya.—Fitowa 34:28; Luka 19:13; Ru’ya ta Yohanna 2:10.

  •   12 Watakila wannan lambar tana nufin cikakken shiri da Allah ya yi. Alal misali, wahayin sama da aka nuna wa manzo Yohanna yana dauke da birni mai “dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu.” (Ru’ya ta Yohanna 21:14; Farawa 49:28) Yin amfani da lambar nan 12, sau da sau yana da ma’ana daya.—Ru’ya ta Yohanna 4:4; 7:4-8, Littafi Mai Tsarki.

  •   40 An yi amfani da lambar nan 40 a lokacin yanka shari’a ko kuma hukunci.—Farawa 7:4; Ezekiyel 29:11, 12.

Hisabi da Lissafi

 Ma’anar lamba a alamance na cikin Littafi Mai Tsarki sun bambanta da hisabi, hakan ta kunshi neman ma’anar lambar ta wurin sihiri da yadda aka hada su da kuma lambar gabaki dayanta. Alal misali, wani boka Bayahude ya yi amfani da lissafi don ya bayyana Nassosin Ibrananci, ya yi amfani da wani boyyayen tsarin lambobi da suka yi daidai da harufa. Hisabi, wani fannin duba ne da Allah ya haramta.—Kubawar Shari’a 18:10-12.