Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki, ana kuma kiransa Nassosi Masu Tsarki, yana ɗauke da maganganu masu hikima. Amma, ka lura da da’awar da Littafi Mai Tsarki ya yi: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah.” (2 Timothawus 3:16) Da akwai tabbaci da yawa game da hakan. Ka bincika waɗannan:

  • Babu wanda ya taɓa yin nasarar ƙalubanci gaskiyar tarihin Littafi Mai Tsarki.

  • Waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki mutane ne masu gaskiya sun rubuta shi da zuciya ɗaya. Gaskiyarsu ta sa rubutun da suka yi ya kasance da gaskiya.

  • Jigon Littafi Mai Tsarki ɗaya ne: kunita ikon da Allah yake da shi na yin sarauta a kan ’yan Adam da kuma cika ƙudurinsa ta wurin Mulkinsa na samaniya.

  • Ko da yake an rubuta shi dubban shekaru da suka wuce, Littafi Mai-Tsarki ba shi da wani kuskure game da wani ra’ayi na tun can dā na kimiyya

  • Tabbaci na tarihi da ke a rubuce sun tabbatar da gaskiyar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki.