Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Karin Jini?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Karin Jini?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu ci jini. Saboda haka, kada mu yarda a yi mana karin jini ko kuma a dafa kamar abinci. Ka yi la’akari da wadannan ayoyin:

  •   Farawa 9:4. Bayan Tufana, Allah ya yarda Nuhu da iyalinsa su ci nama amma ya ce kada su ci jini. Allah ya ce wa Nuhu: “Sai dai nama tare da ransa, watau jininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba.” Wannan dokar ta shafi kowane mutum daga zamanin Nuhu har zuwa yanzu da yake mu daga zuriya ɗaya muka fito.

  •   Levitikus 17:14. “Ba za ku ci jini na kowane irin nama: gama ran dukan nama shi ne jininsa: dukan wanda ya ci shi za a datse shi.” A gaban Allah, rai da jini daya ne kuma na shi ne. Ko da yake wannan doka an ba wa al’ummar Isra’ila ce kawai, duk da haka, dokar ta nuna muhimmancin yadda Allah yake ji game da cin jini.

  •   Ayyukan Manzanni 15:20. “Hanu daga . . . jini.” Allah ya ba Kiristoci doka iri daya da ya ba Nuhu. Tarihi ya nuna cewa Kiristoci na farko sun ki su ci jini ko kuma su yi amfani da shi don jinya.

Me ya sa Allah ya umurce mu mu guji karin jini?

 Da akwai dalilai masu kyau da suka nuna cewa karin jini ba shi da kyau ga lafiyar jiki. Mafi muhimmanci ma shi ne Allah ya ce mu guji karin jini domin abin da jini yake wakilta yana da tsarki a gare shi.—Levitikus 17:11; Kolosiyawa 1:20.