Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Littafin Bature Ne?

Littafi Mai Tsarki Littafin Bature Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Ba turawa ba ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki. Dukan mutanen da Allah ya sa su rubuta Littafi Mai Tsarki daga Asiya suka fito. Littafi Mai Tsarki ba ya daraja wata al’umma fiye da wata. Ya ce: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.