Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Yadda Za Mu Kaunaci Kanmu?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Yadda Za Mu Kaunaci Kanmu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana da kyau kuma ya dace mu so kanmu, amma kar ya wuce kima. Hakan yana nufin cewa mu rika kula da kanmu da daraja kanmu kuma mu rika kāre mutuncinmu. (Matiyu 10:31) Littafi Mai Tsarki bai ce mu rika son kanmu fiye da kome ba, amma ya nuna mana yadda za mu kaunaci kanmu daidai ruwa daidai gari.

Wa ya kamata mu nuna wa kauna da farko?

  1. Allah ne ya kamata mu fara nuna wa kauna. Littafi Mai Tsarki ya ce doka mafi girma ita ce: “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka.”​— Markus 12:28-30; Maimaitawar Shari’a 6:5.

  2. Doka ta biyu mafi muhimmanci ita ce: “Ka kaunaci makwabcinka kamar yadda kake kaunar kanka.”—Markus 12:31; Littafin Firistoci 19:18.

  3. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai fito gar da gar ya ce mu kaunaci kanmu ba, amma tun da yake ya ce ‘Ka kaunaci makwabcinka kamar yadda kake kaunar kanka,’ hakan ya nuna cewa ba laifi ba ne idan muna kauna da kuma daraja kanmu yadda ya kamata.

Wane ne Yesu ya fi kauna?

Yesu ya nuna mana yadda za mu kaunaci Allah da makwabtanmu da kuma kanmu, kuma ya umurci mabiyansa su bi misalinsa.​—Yohanna 13:34, 35.

  1. Yesu ya kaunaci Allah sosai fiye da kome kuma ya mai da hankali sosai sa’ad da yake yin aikin da Allah ya ba shi. Ya ce: “Ina yin daidai abin da Uba ya fada mini in yi ne domin duniya ta sani ina kaunar Uban.”—Yohanna 14:31.

  2. Yesu ya kaunaci makwabtansa kuma ya nuna hakan ta wajen kula da bukatunsu. Mafi muhimmanci ma, ya ba da ransa a madadin su.​—Matiyu 20:28.

  3. Yesu yana kaunar kansa, shi ya sa ya dauki lokaci don ya huta, ya ci abinci kuma ya yi sha’ani da mabiyansa da kuma almajiransa.​—Markus 6:31, 32; Luka 5:29; Yohanna 2:1, 2; 12:2.

Shin idan kana kaunar mutane fiye da kanka, hakan zai hana ka farin ciki ne ko ya zubar da mutuncinka?

A’a, domin an halicce mu a kamanin Allah, wanda kauna ce abu mafi muhimmanci a gare shi. (Farawa 1:27; 1 Yohanna 4:8) Hakan na nufin cewa mu ma muna iya kaunar mutane. Ba laifi ba ne mu kaunaci kanmu, amma za mu yi farin ciki sosai idan muna kaunar Allah kuma muna yi wa mutane alheri. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”—Ayyukan Manzanni 20:35.

Mutane da yawa a yau sun ce mutum zai fi farin ciki idan yana kaunar kansa fiye da kome. A wajen su, ‘kaunar kanmu’ ya maye gurbin ‘kaunar makwabtanmu.’ Amma labarai da yawa sun nuna cewa mutum zai fi samun koshin lafiya da kuma farin ciki idan yana bin shawarar Littafi Mai Tsarkin nan da ya ce: “Kada ka yi wa kanka kadai abu mai kyau, amma ka yi wa dan’uwanka kuma.”—1 Korintiyawa 10:24.