Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah Ce?

Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah Ce?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Marubutan Littafi Mai Tsarki da yawa sun ce Allah ne ya ja-goranci abin da suka rubuta. Ka lura da waɗannan misalai:

  •  Sarki Dauda: “Ruhun Ubangiji ya yi zance da ni, Maganatasa kuma tana bisa harshena.”—2 Samuila 23:1, 2.

  •  Annabi Ishaya: “In ji Ubangiji, Ubangiji mai-runduna.”—Ishaya 22:15.

  •  Manzo Yohanna: “Ru’ya ta Yesu Kristi, wanda Allah ya ba shi.”—Ru’ya ta Yohanna 1:1.