Koma ka ga abin da ke ciki

Yesu Ya Tashi daga Mutuwa da Jiki na Zahiri ne ko na Ruhu?

Yesu Ya Tashi daga Mutuwa da Jiki na Zahiri ne ko na Ruhu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce an kashe Yesu ‘cikin jiki, amma an rayar [an tayar] da shi cikin ruhu.’—1 Bitrus 3:18; Ayyukan Manzanni 13:34; 1 Korintiyawa 15:45; 2 Korintiyawa 5:16.

Abin da Yesu ya fada ya nuna cewa ba za a ta da shi da jiki na zahiri ba. Ya ce zai ba da jikinsa “sabili da ran duniya,” wato don ya fanshe ’yan Adam. (Yohanna 6:51; Matta 20:28) Da a ce ya tashi da jikinsa na zahiri, da mutuwarsa bai fanshi ’yan Adam ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ya ba da jikinsa da jininsa hadaya “so daya dungum.”—Ibraniyawa 9:11, 12.

Da yake an ta da Yesu da jiki na ruhu, ta yaya almajiransa suka gan shi?

  • Halittu na ruhu suna iya canja siffarsu zuwa na ’yan Adam. Alal misali, mala’iku su yi hakan a dā, har ma sun ci abinci tare da ’yan Adam. (Farawa 18:1-8; 19:1-3) Amma, su mala’iku ne har ila, suna iya komawa jikinsu na ruhu kuma su bace.—Alkalawa 13:15-21.

  • Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya dauki siffar ’yan Adam na dan lokaci kamar yadda mala’iku suka yi a dā. Amma da yake shi ruhu ne, yana iya bacewa kuma ya sake bayyana nan da nan. (Luka 24:31; Yohanna 20:19, 26) Ya bayyana sau da yawa kuma ya yi hakan da kamanni dabam-dabam. Shi ya sa almajiransa ba su gane shi da farko ba. Bayan sun ji muryarsa kuma sun ga abin da ya yi ne suka gane cewa Yesu ne.—Luka 24:30, 31, 35; Yohanna 20:14-16; 21:6, 7.

  • Sa’ad da Yesu ya bayyana ga manzo Toma, ya yi amfani da jiki mai rauni. Yesu ya yi hakan saboda ya karfafa bangaskiyar Toma wanda ya yi shakka cewa and ta da Yesu.—Yohanna 20:24-29.