Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Iyalina ta Kasance da Farin Ciki Kuwa?

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Iyalina ta Kasance da Farin Ciki Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Hakika. Ga wasu shawarwari masu kyau da ke Littafi Mai Tsarki da suka taimaka wa miliyoyin mutane maza da mata su sami farin ciki a iyalansu:

  1.   Ku yi aure bisa doka. Za ku yi zaman lafiya da iyalinku idan kuka yi aure bisa doka.—Matta 19:4-6.

  2.   Ku yi kaunar juna kuma ku daraja juna. Hakan yana nufin cewa za ku bi da juna yadda kuke so a bi da ku.—Matta 7:12; Afisawa 5:25, 33.

  3.   Ku guji yin ashar. Ku kasance da halin kirki idan kuka bata wa juna rai. (Afisawa 4:31, 32) Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce a Misalai 15:1: “Mayar da magana da taushi ya kan juyar da hasala: Amma magana mai-zafi ta kan ta da fushi.”

  4.   Kada ku ci amanar juna. Bari soyayya da jima’i ya kasance tsakanin ku biyu kadai. (Matta 5:28) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane, gado kuma shi kasance mara-kazanta.”—Ibraniyawa 13:4.

  5.   Ku horar da ’ya’yanku cikin kauna. Kada ku yi sake ko kuma ku riƙa hasala musu.—Misalai 29:15; Kolosiyawa 3:21.