Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya ce Game da Euthanasia, Wato Daukan Ran Wadanda Suke Shan Azaba Don Ciwo?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya ce Game da Euthanasia, Wato Daukan Ran Wadanda Suke Shan Azaba Don Ciwo?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki bai yi magana game da batun daukan ran wanda ke shan mummunar azaba sanaddiyar ciwo ba. a Duk da haka, abin da ya fada game da rai da kuma mutuwa zai taimaka mana mu fahimci batun. Bai dace mutumin ya dauki ran wani ba. kuma ba wata ka’ida cewa a yi kokarin taimaka wa mutum ko ta yaya don ya ci gaba da rayuwa yayin da yake fama da ciwon ajali.

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Allah shi ne Mahalicci “mafarin rai.” (Zabura 36:9; Ayyukan Manzanni 17:28) A wurin Allah, rai abu mai tamani ne. Saboda da haka, Allah na tir da wanda ya yi kisa ko kuma wanda ya kashe kansa. (Fitowa 20:13; 1 Yohanna 3:​15) Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar mu rika dauka matakai don mu kare ranmu da kuma rayukan wadansu. (Maimaitawar Shari’a 22:8) Babu shakka, Allah na so su rika daraja rai.

Sa’ad da mutum yake da ciwon ajali fa?

 Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan daukan ran mutum ba ko da mutumin yana fuskantar ciwon da zai yi ajalinsa. Misalin Sarki Saul na Isra’ila ya nuna hakan. A lokacin da aka ji masa rauni a bakin daga, Saul ya gaya wa bawansa ya dauki ransa. (1 Sama’ila 31:3, 4) Bawan ya ki yin abin da Saul ya ce. Daga baya wani mutum ya yi karya cewa shi ne ya aikata umurnin Saul. Dauda wanda ke da ra’ayin Allah game da rai, ya hukunta mutumin cewa ya yi kisan kai.—2 Sama’ila 1:6-16.

Dole ne a yi kokarin dada tsawon rai ko ta yaya?

 Yayin da mutuwa ta zama tabbas, Littafi Mai Tsarki bai bukaci a yi kokarin dada tsawon lokacin mutuwar ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ya dace. Mutuwa babban abokin gabarmu ne. Kuma mutuwa sakamakon zunubi ne da muka gāda. (Romawa 5:12; 1 Korintiyawa 15:26) Amma kar mu ji tsoron mutuwa, domin Allah ya yi alkawarin tayar da wadanda suka mutu. (Yohanna 6:39, 40) Mutumin da ya daraja rai zai nemi hanyar yin jinya da ta dace da zai iya samu. Duk da haka, mutum ba ya bukatar zabar hanyar yin jinya da za ta kara tsawon yanayin mutuwa yayin da mutuwar ta yi kusa sosai.

Kashe kai laifi ne da ba za a gafarta ba?

 A’a, Littafi Mai Tsarki bai lissafta yin kisan kanka a matsayin zunubi da ba za a gafarta ba. Ko da yake yin kisan kanka zunubi ne mai girma, b Allah ya san yanayoyin kamar hauka da alhini da ta wuce gona da iri ko kuma wadansu halaye da ake gādan su da za su iya kai mutum ga daukan ransa. (Zabura 103:13,14) Ta Littafi Mai Tsarki Allah yana kwantar da hankalin wadanda ke shan wahala. Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce, “za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Wannan ya nuna cewa akwai begen ta da mutanen da suka yi mummunar kuskure kamar daukan ransu.

a Mutanen da Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa sun dau ransu, mutane ne da ba su kiyaye dokokin Allah ba.—2 Sama’ila 17:23; 1 Sarakuna 16:18; Matiyu 27:3-5.

b Kamus mai suna Merriam-Webster Learner’s Dictionary ya ba da ma’ana kalmar nan Euthanasia cewa yana nufin “daukan rai domin tausayi mutumin da ke shan azaba don ciwon ko kuma rauni da ba za a iya warkarwa ba don a rage masa wahala. Yayin da likita ya taimaka ma wani ya dau ransa domin azaba, ana kiran hakan kisan kai na mai ciwo da taimakon likita.