Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ƙirgen Littafi Mai Tsarki ya Bayyana Game da Shekara ta 1914?

Mene ne Ƙirgen Littafi Mai Tsarki ya Bayyana Game da Shekara ta 1914?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kirgen kwanakin Littafi Mai Tsarki, ya nuna cewa an kafa Mulkin Allah a sama a shekara ta 1914. Mun ga tabbacin hakan a cikin annabcin da aka rubuta a Littafin Daniyel sura 4.

 Takaitaccen Annabcin. Allah ya sa Nebuchadnezzar Sarkin Babila ya yi mafarkin wani babban itace da aka tsare shi. An hana gindin sawayen wannan itacen girma har na tsawon “lokatai guda bakwai,” amma itacen ya sake girma bayan wadannan lokatan.—Daniyel 4:1, 10-16.

 Cikar annabcin na farko. Babban itacen na wakiltar Sarki Nebuchadnezzar. (Daniyel 4:20-22) An ‘tsare shi’ a alamance sa’ad da ya haukace kuma ya rasa sarautarsa na tsawon shekaru bakwai. (Daniyel 4:25) Bayan wannan, Allah ya sa Nebuchadnezzar ya warke kuma ya sake soma sarauta. Hakan ya sa ya girmama sarautar Allah.—Daniyel 4:34-36.

 Tabbaci da ya nuna cewa annabcin yana da cikawa na biyu mai muhimmanci. Ainihin manufar annabcin shi ne don “masu-rai su sani Madaukaki yana rike da sarauta a cikin mulkin mutane, yana bayar ga wanda ya ga dama, yana sarautar da kaskantattun mutane kuma.” (Daniyel 4:17) Shin Nebuchadnezzar mai girman kai ne Allah yake so ya ba wa wannan sarautar? A’a, domin Allah ya riga ya sa Nebuchadnezzar ya yi wani mafarki da ya nuna cewa ba za a ba shi wannan sarautar ko kuma a ba wa wani dan siyasa ba. Maimakon haka, Allah “za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba dadai.”—Daniyel 2:31-44.

 A dā, Allah ya kafa wani mulki da ke sarauta bisa duniya a madadinsa: wato al’ummar Isra’ila ta dā. Allah ya kyale an “halaka” wannan mulkin domin masarautan ta sun yi rashin aminci, amma ya annabta cewa zai ba da mulkin ga “mai shi.” (Ezekiel 21:25-27, Littafi Mai Tsarki) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ne wanda ya cancanci a ba shi wannan mulkin da zai dawwama. (Luka 1:30-33) Yesu ba kamar Nebuchadnezzar yake ba, shi “mai kaskantar zuciya ne” kamar yadda aka annabta.—Matta 11:29.

 Mene ne itace da ke littafin Daniyel sura 4 ke wakilta? A wasu yanayoyi, itace na wakiltar sarauta a cikin Littafi Mai Tsarki. (Ezekiel 17:22-24; 31:2-5) Babban itacen annabcin da ke Daniyel sura 4 na wakiltan sarautar Allah a cikarsa na biyu mai muhimmanci.

 Mene ne tsare itacen ke wakilta? Kamar yadda tsare itacen na wakiltar dakatar da sarautar Nebuchadnezzar a cikar annabcin na farko, hakan nan ma a cikawa ta biyu, tsare itacen na wakiltar dakatar da sarautar Allah a duniya. Wannan ya faru ne sa’ad da Nebuchadnezzar ya halaka Urushalima, inda sarakunan Isra’ila suka zauna bisa ‘kursiyin Jehobah’ a matsayin wakilan Allah.—1 Labarbaru 29:23.

 Mene ne “lokatai guda bakwai” din ke wakilta? “Lokatai guda bakwai” din suna wakiltar lokacin da Allah ya kyale mutanen al’umma su yi sarauta bisa duniya. Wannan “lokatai guda bakwai” din sun soma ne a watan Oktoba a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu, sa’ad da ’yan Babila suka halaka Urushalima bisa ga kirgen Littafi Mai Tsarki.  a2 Sarakuna 25:1, 8-10.

 Yaya ne tsawon “lokatai guda bakwai” din? Ba tsawon shekaru bakwai ne kawai kamar na Nebuchadnezzar ba. Yesu ya ba da amsar wannan tambayar sa’ad da ya ce “al’ummai za su tattake Urushalima [wato sarautar Allah] kuma har zamanan Al’ummai sun cika.” (Luka 21:24) Wannan “zamanan al’ummai,” wato lokacin da Allah ya kyale “al’ummai” su tattake sarautarsa daya suke da “lokatai guda bakwai” na littafin Daniyel sura 4. Hakan yana nufin cewa “lokatai guda bakwai” din ba su cika ko ba har lokacin da Yesu yake duniya.

 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu san tsawon wadannan “lokatai guda bakwai.” Ya ce, “lokatai” uku da rabi, kwanaki 1,260 ne. Saboda haka, lokatai uku da rabi sau biyu zai kai mu ga samun kwanaki 2,520. (Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14) Idan muka yi amfani da annabcin Littafi Mai Tsarki na “shekara guda maimakon kowace rana,” kwanaki 2,520 zai kai mu ga samun shekaru 2,520. Saboda wannan kirgen, “lokatai guda bakwai” din ko kuma shekaru 2,520 sun kare a watan Oktoba shekara ta 1914.—Litafin Lissafi 14:34; Ezekiel 4:6.

a Don ƙarin bayani a kan dalilin da ya sa aka yi amfani da kwanan watan nan 607, ka duba talifofin nan “When Was Ancient Jerusalem Destroyed?​—Part One,” (Yaushe ne Aka Halaka Urushalima a Zamanin Dā—Sashe na Ɗaya) a shafuffuka na 26-​31 na Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2011, da “When Was Ancient Jerusalem Destroyed?​—Part Two” (Yaushe ne Aka Halaka Urushalima a Zamanin Dā—Sashe na Biyu) a shafuffuka na 22-​28 a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2011.