Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bala’i?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bala’i?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Ba Allah ba ne ke jawo bala’i da ke faruwa a yau, amma yana jin tausayin wadanda bala’i ya shafa. Mulkin Allah zai kawar da dukan abubuwan da ke sa mutane shan wahala, har da bala’i. Kafin wannan lokacin, Allah yana karfafa wadanda bala’i ya shafa.​—2 Korintiyawa 1:3.

 Ta yaya muka san cewa Allah ba ya yin amfani da bala’i don yi wa mutane horo?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya yi amfani da ruwa da wuta da sauransu don ya yanke hukunta mugaye, amma bai yi hakan yadda bala’i ke yi a yau ba.

  •   Bala’i yana kashe da kuma nakasa kowanne mutum. Amma Allah yana tabbata cewa mugaye ne kawai za su halaka sa’ad da ya yi amfani da bala’i don ya halaka mugaye. Alal misali, Lutu da ’ya’yansa mata biyu sun tsira sa’ad da Allah ya halaka biranen Saduma da Gwamarata. (Farawa 19:​29, 30) Allah ya san zuciyar mutanen zamanin kuma ya halaka wadanda ainihin mugaye ne.​—Farawa 18:​23-32; 1 Sama’ila 16:7.

  •   Bala’i yana faruwa farat daya. Amma, Allah yana yi wa mugaye gargadi kafin ya yi amfani da bala’i ya halaka su. Wadanda suka bi gargadinsa suna da zarafin tsira wa masifar.​— Farawa 7:​1-5; Matiyu 24:​38, 39.

  •   ’Yan Adam ne suke jawo wasu bala’in. Ta yaya? Suna bata mahalli kuma suna gini a wuraren da za a iya yin girgizar kasa da ambaliya da kuma canjin yanayi. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18) Allah bai da laifi sa’ad da ’yan Adam suka yi kuskure kuma aka samu mugun sakamako don haka.​—Karin Magana 19:3.

 Shin bala’i alama ne cewa muna kwanaki na karshe?

 E, annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun ce za a yi bala’i a “karshen zamani” ko kuma “kwanakin karshe.” (Matiyu 24:3; 2 Timoti 3:1) Alal misali, Yesu ya ce: “Za a kuma yi yunwa da rawar ƙasa a wurare dabam-dabam.” (Matiyu 24:7) Nan ba da dadewa ba, Allah zai kawar da dukan abubuwa da ke jawo bakin ciki da wahala, har da bala’i.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4.

 Ta yaya Allah yake taimaka wa mutanen da bala’i ya shafa?

  •   Allah yana karfafa su da Kalmarsa. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Allah ya damu da mu kuma yana bakin ciki sa’ad da muke shan wahala. (Ishaya 63:9; 1 Bitrus 5:​6, 7) Kalmarsa ta kuma ambata alkawarin da ya yi cewa lokaci na zuwa da bala’i ba zai kara aukuwa ba.​—Ka duba “ Nassosin da za su karfafa mutanen da bala’i ya shafa.”

  •   Allah yana yin amfani da bayinsa don ya karfafa mutanen da bala’i ya shafa. Allah yana sa bayinsa a duniya su yi koyi da Yesu. An annabta a cikin Littafi Mai Tsarki cewa Yesu zai karfafa “wadanda suka fid da zuciya” da “dukan masu baƙin ciki.” (Ishaya 61:​1, 2) Masu bauta wa Allah suna kokari su yi hakan.​—Yohanna 13:15.

     Allah yana amfani da bayinsa don ya taimaka wa mutanen da bala’i ya shafa.​—Ayyukan Manzanni 11:​28-30; Galatiyawa 6:10.

Shaidun Jehobah suna taimaka ma wadanda mahaukaciyar gugguwa mai dauke da ruwa ta shafa a Puerto Rico

 Shin ka’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu yi shiri don bala’i?

 E. Ko da yake ba a rubuta Littafi Mai Tsarki don sa mu yi shirin bala’i ba, amma yana dauke da ka’idodin da za su taimaka mana. Alal misali:

  •   Ka yi shirin abin da za ka yi idan bala’i ya faru. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce.” (Karin Magana 22:3) Ya dace mu tsai da shawarar abin da za mu yi tun da wuri kafin mu shiga tsaka mai wuya. Yin hakan ya kunshi tattara abubuwan da ka riga ka ajiye da za ka dauka cikin sauki a lokacin gaggawa da kuma tattauna da iyalinka wurin da za ku hadu idan bala’i ya auku.

  •   Ranka ya fi dukiya muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba mu shigo cikin duniya da kome ba, haka ma ba za mu iya fita cikinta da kome ba.” (1 Timoti 6:​7, 8) Ya kamata mu kasance a shirye mu bar gidanmu da dukiyarmu domin mu tsira. Muna bukatar mu tuna cewa ranmu ya fi abin duniya muhimmanci.​—Matiyu 6:25.