Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ake Nufi da Alamun “Kwanaki na Karshe” ko ‘Karshen Duniya”?

Mene ne Ake Nufi da Alamun “Kwanaki na Karshe” ko ‘Karshen Duniya”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abubuwa dabam-dabam da za su nuna cewa an kai “cikar zamani” ko kuma ‘karshen duniyar’ nan. (Matta 24:3) Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lokacin “kwanaki na karshe.” (2 Timotawus 3:1; Daniyel 8:19) Ga wasu abubuwa da za su faru a kwanaki na karshe:

 • Za a yi yaki a wurare da yawa a duniya.—Matta 24:7; Ru’ya ta Yohanna 6:4.

 • Yunwa.—Matta 24:7; Ru’ya ta Yohanna 6:5, 6.

 • Manya-manyan girgizar kasa.—Luka 21:11.

 • Cututtuka ko kuma annoba.—Luka 21:11.

 • Mugunta za ta karu.—Matta 24:12.

 • Yin abubuwan da suke gurbata duniya.—Ru’ya ta Yohanna 11:18.

 • Halayen mutane za su dada muni kuma za su zama “marasa godiya, marasa tsarki, . . . masu bata sunayen wadansu, marasa kame kansu, marasa tausayi, masu kin nagarta, masu cin amana, marasa hankali, masu cika da daga kai.”—2 Timotawus 3:1-4, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

 • Rashin zaman lafiya a cikin iyalai domin mutane sun zama “marasa kauna irin na tabi’a,” kuma yara ba sa ‘bin iyayensu.’—2 Timotawus 3:2, 3.

 • Yawancin mutane za su daina bauta wa Allah.—Matta 24:12.

 • Mutane da yawa za su yi kamar suna bauta wa Allah.—2 Timotawus 3:5.

 • Za a sami karin haske game da annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, har da wadanda suka shafi kwanaki na karshe.—Daniyel 12:4.

 • Za a yi wa’azin bisharar Mulki a dukan duniya.​—Matta 24:14.

 • Mutane da yawa za su ki su yarda cewa karshe ya kusa.—Matta 24:37-39; 2 Bitrus 3:3, 4.

 • Yadda dukan annabce-annabcen nan za su cika a lokaci daya.​—Matta 24:33.

Shin muna “kwanaki na karshe” kuwa?

E. Yanayin da duniya take ciki da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya fada, sun tabbatar da cewa kwanakin karshe sun soma ne a shekara ta 1914. A lokacin ne aka kafa Mulkin Allah a sama kuma abu na farko da sarkin ya yi shi ne, ya kori Shaidan Iblis da aljannunsa daga sama zuwa duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) Munanan abubuwan da ke faruwa a duniya sun nuna cewa Shaidan ne yake da tasiri a kan ’yan Adam shi ya sa ’yan Adam suke ‘shan wahala sosai’ kuma rayuwa take da wuya.—2 Timotawus 3:1, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.