Koma ka ga abin da ke ciki

An Canja Ko Kuma Sake Sakon Littafi Mai Tsarki Ne?

An Canja Ko Kuma Sake Sakon Littafi Mai Tsarki Ne?

A’a. Domin binciken rubuce-rubuce na dā da aka yi ya nuna cewa duk da kofan Littafi Mai Tsarki a kan abubuwan da ke iya lalacewa, babu abin da ya canja ainihin saƙon da ke ciki.

Shin hakan na nufin cewa ba a taɓa yin kuskure a wajen kofansa ba?

An gano dubban rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Akwai bambanci cikin wasunsu, hakan yana nufin cewa an yi wasu kurakurai yayin da ake kofansu. Yawancin bambancin bai taki kara ya karye ba balle ya canja ma’anar ayar. Amma kuma, an gano wasu bambanci masu muhimmanci, kuma da gangan aka yi su da dadewa domin a canja sakon Littafi Mai Tsarki. Ga misalai biyu:

  1. A littafin 1 Yohanna 5:​7, wasu fassarar Littafi Mai Tsarki da aka yi dā sun kunshi wadannan kalmomin: ‘a sama, Uban, da Kalmar, da kuma Ruhu Mai Tsarki: kuma dukansu ukun daya ne.’ Amma kuma, rubuce-rubuce na dā sun tabbatar da cewa babu wadannan kalmomin a cikin rubutu na asali. Daga baya ne aka dada su. * Shi ya sa aka cire su daga cikin fassarar Littafi Mai Tsarki na yanzu.

  2. Sunan Allah ya bayyana sau dubbai a cikin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Duk da haka, yawancin fassarar Littafi Mai Tsarki sun sauya sunan da lakabi kamar su “Ubangiji” ko kuma “Allah.”

Ta yaya za mu iya tabbatar da cewa ba za a sāke samun kurakurai da yawa kuma ba?

A yanzu dai, an samo rubuce-rubuce na dā da yawa da zai taimaka a iya gano kurakuran. * Ta yaya bincikan wadannan littattafan ya nuna cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki babu kuskure a yau?

  • Da yake magana game da rubutun da ke cikin Nassosin Ibrananci (wanda ake kira “Tsohon Alkawari”), wani masani mai suna Willaim H. Green, ya ce: “Babu wani aiki na dā da aka kofa da kyau ba tare da kuskure ba kamar wannan.”

  • Wani masani mai suna F. F. Bruce, bayani game da Nassin Helenanci na Kirista, ko kuma “Sabon Alkawari,” cewa: “Tabbacin da muke da shi cewa babu kuskure a rubutun Sabon Alkawari yana da yawa fiye da rubuce-rubucen wasu sanannun marubuta, kuma babu wanda zai iya musanta hakan.”

  • Wani mai suna Sir Frederic Kenyon, da ya san game da rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum zai iya daukan Littafi Mai Tsarki a hannunsa ya kuma ce ba tare da tsoro ko shakka ba cewa yana rike da Kalmar Allah ta gaskiya, wanda yana nan kamar yadda yake babu abin da aka cire tun daga zamanin dā har zuwa zamaninmu.”

Wane Karin dalilai da kuma tabbaci ne suka nuna cewa ba a cire wani abu daga Littafi Mai Tsarki ba?

  • Marubutan Yahudawa da na Kirista sun adana labaran da suka nuna kurakuran da mutanen Allah suka yi. * (Littafin Lissafi 20:12; 2 Samai’ila 11:​2-4; Galatiyawa 2:​11-​14) Ban da haka ma, sun adana wuraren da aka rubuta rashin biyayyar da Yahudawa suka yi wa Allah kuma hakan ya nuna koyarwar da mutane suka kago. (Hosiya 4:2; Malakai 2:​8, 9; Matta 23:​8, 9; 1 Yohanna 5:​21) Da yake sun kofa labaran nan daidai yadda suke, marubutan sun nuna cewa suna da gaskiya kuma sun daraja Maganar Allah.

  • Allah ne ya hure rubutun Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya tabbatar cewa zai kare koyarwar da ke ciki. * (Ishaya 40:8; 1 Bitrus 1:​24, 25) Domin yana so dukan mutane su amfana daga Littafi Mai Tsarki. (1  Korintiyawa 10:11) Hakika, dukan “abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin hakuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.”​—Romawa 15:4

  • Yesu da mabiyansa sun yin kaulin Nassosin Ibrananci ba tare da wani shakka game da gaskiyar rubutun ba.​—Luka 4: ​16-​21; Ayyukan Manzanni 17: ​1-3

^ sakin layi na 3 Babu wadannan kalmomin a cikin Codex Sinaiticus da Codex Alexandrinus da Vatican Manuscript 1209 da Latin Vulgate na ainihi da Philoxenian-Harclean Syriac Version, ko kuma the Syriac Peshitta.

^ sakin layi na 5 Alal misali, an gano rubuce-rubuce sama da 5,000 a Hellenanci ko kuma Sabon Alkawari kamar yadda ake kira, ko kuma Nassin Helenanci na Kirista.

^ sakin layi na 9 Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa wakilan Allah ba sa kuskure ba. Amma ya nuna dalla-dalla cewa: “Babu mutumin wanda ba shi yin zunubi.”​—1 Sarakuna 8:​46.

^ sakin layi na 10 Littaffi Mai Tsarki ya ce ko da yake Allah bai furta musu kalmomin da za su rubuta ba, ya tabbatar da cewa mutanen sun rubuta abin da yake so.​—2 Timotawus 3:​16, 17; 2 Bitrus 1:​21.