Koma ka ga abin da ke ciki

A Ina ne Kayinu Ya Sami Matarsa?

A Ina ne Kayinu Ya Sami Matarsa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Dan farin iyayenmu na farko, wato Kayinu ya auri daya daga cikin kannensa mata ko kuma danginsa. Mun fahimci hakan ne ta wurin bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da Kayinu da kuma danginsa.

Gaskiya game da Kayinu da kuma danginsa

  • Dukan ‘yan Adam ‘ya’yan Adamu da Hawwa’u ne. Allah “ya halicci dukan al’umma daga mutum guda [Adamu], domin su zauna a dukan fuskar duniya.” (Ayyukan Manzanni 17:​26, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Matar Adamu, wato Hawwa’u ita ce “uwar masu rai duka.” (Farawa 3:20) Saboda haka, Kayinu ya auri daya daga cikin kannensa.

  • Kayinu da dan’uwansa Habila suna cikin yaran farko da Hawwa’u ta haifa. (Farawa 4:​1, 2) A lokacin da aka kori Kayinu don ya kashe dan’uwansa, Kayinu ya ce, duk “wanda ya same ni za ya kashe ni.” (Farawa 4:14) Su waye ne Kayinu ya ji tsoronsu? Littafi Mai Tsarki ya ce Adamu ‘ya kuma haifi ‘ya’ya maza da mata.’ (Farawa 5:4) Da alama wasu yaran Adamu da Hawwa’u sun sa Kayinu a gaba shi ya sa yake tsoronsu.

  • A dā, mutane suna iya auran danginsu. Alal misali, Ibrahim ya auri ‘yar matar babansa. (Farawa 20:12) Amma an fara haramta irin wannan auren a lokacin da aka ba da Doka ta hannun Musa kuma hakan ya faru ne shekaru da yawa bayan zamanin Kayinu. (Levitikus 18:​9, 12, 13) Da alama a lokacin idan mutum ya auri ‘yar’uwarsa kuma suka haihu, yaran ba sa samun lahani kamar yadda ake gani a yanzu.

  • Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin Adamu da Hawwa’u da iyalinsa daidai yadda ya faru. Ba littafin Farawa da Musa ya rubuta ba ne kawai ya ba da labarin zuriyar Adamu dalla-dalla, wasu ‘yan tarihi ma kamar su Ezra da Luka sun yi hakan. (Farawa 5:​3-5; 1 Labarbaru 1:​1-4; Luka 3:38) Marubutan Littafi Mai Tsarki ma sun ambaci labarin Kayinu a matsayin abin da ya faru a dā.​—Ibraniyawa 11:4; 1 Yohanna 3:12; Yahuda 11.