Koma ka ga abin da ke ciki

Abubuwan da Za Su Taimaka Maka

Ka koyi abubuwa da kuma halayen da kake bukata don ka zama mutum nagari a nan gaba.

Controlling Emotions

Ta Yaya Zan Rika Bi da Yadda Nake Ji?

Canjin yadda mutum yake ji ba sabon abu ba ne amma matasa suna rudewa idan suka ga hakan na faruwa da su. Abin farin ciki shi ne, akwai mafita don za ka iya magance irin matsalar idan kana fama da ita.

Yaya Zan Bi da Yadda Nake Ji a Hanyar da Ta Dace?

An shirya wannan shafin rubutun ne don ya taimaka maka ka bi da matsalolinka a hanyar da ta dace.

Ta Yaya Zan Guji Mugun Tunani?

Za ka iya kasancewa da ra’ayin da ya dace ta wajen bin wadannan shawarwari.

Me Zan Yi Idan Bala’i Ya Fado Mini?

Wasu matasa sun ba da labarin abin da ya taimaka musu su jure.

Time and Money

Ta Yaya Zan Guji Kasala?

Me zai iya sa ka shiga wannan yanayin? Shin kana ganin cewa za ka kasala don ayyuka da yawa? Idan haka ne, to me za ka yi game da hakan?

Ta Yaya Zan Daina Yin Shiririta?

Ga taimako a kan yadda za ka iya daina yin shiririta!

Matasa Suna Magana Game da Kudi

Ka nemi taimako a kan yadda za ka yi ajiyar kudi da yin amfani da kudi da kuma irin fifikon da za ka ba kudi a rayuwarka.

Me Zai Taimaka Maka Ka Rage Kashe Kudi?

Ka taba shiga wani shago don ka yi kallo kawai amma da ka tashi fitowa sai ka saya wani abu mai tsada? Idan e ce amsarka, wannan talifin zai taimaka maka.

Hanyar da Ta Dace Ka Yi Amfani da Kudinka

Ka yi amfani da wannan shafin rubutun ka gwada yawan abin da kake bukata da abin da kake so don ka ga yadda hakan zai daidai da kudin da za ka kashe.

Personal Development

Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Ka Rika Fadin Gaskiya?

Shin wadanda suke karya da sata suna amfana sosai?

Kai Mai Gaskiya Ne?

Ka bincika kanka a wannan jarabawa mai sassa uku.

Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?

Ka ga fannoni uku da na’urori za su iya hana ka natsuwa, da abin da zai taimaka maka ka iya mai da hankali ga abin da kake yi.

Me Ya Sa Koyan Wani Yare Yake da Muhimmanci?

Wadanne kalubale suke fuskanta sa’ad da suke yin hakan? Wadanne albarka ake samu a yin hakan?

Shawara don Koyan Wani Yare

Koyan wani yare yana bukatar kokari da lokaci da kuma kwazo. Wannan shafin rubutun zai taimaka maka ka tsara yadda za ka koyi wani yare ba tare da matsala ba.

A Shirye Na Ke In Bar Gida?

Wadanne tambayoyi ne ya kamata ka yi la’akari da su kafin ka dau irin wannan mataki mai muhimmanci?

Social Life

Me Zan Yi Don In Rage Jin Kunya?

Kada ka bar damar yin abokan kirki da kuma jin dadin wasu abubuwa a rayuwa ta wuce ka.

Nuna Ladabi Yana da Muhimmanci Kuwa?

Tsohon yayi ne ko kuwa ba shi da muhimmanci?

Me Ya Sa Ya Dace In Nemi Gafara?

Ka bincika dalilai uku da suka sa ya kamata ka nemi gafara ko da kana ganin ba kai ne mai laifi ba.

Idan Abokina Ya Bata Mini Rai Kuma Fa?

Kana bukatar ka san cewa babu wata dangantaka tsakanin ’yan Adam da ba a samun matsala. Amma mene ne za ka yi idan abokinka ya yi ko kuma fadi abin da ya bata maka rai?

Me za ka yi idan an zolaye ka?

Wadanda ake yi musu zolaya suna ganin kamar ba su da karfi. Wannan talifin yana bayyana yadda za a iya magance wannan yanayi.

Ka Bugi Azzalumi Ba Tare da Damtse Ba

Ka koyi abin da ya sa ake cin zali da kuma abin da za ka yi idan aka ci zalinka.