Koma ka ga abin da ke ciki

Umurni don Nazari

Ka saukar da wannan umurni don nazari, kuma ka yi amfani da shi da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ka bincika abin da ka yi imani da shi, kuma ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar don ka iya bayyana ma wasu abin da ka yi imani da shi.

BABI NA 1

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?—(Sashe na 1)

Me za ka ce idan wani ya ce maka “Allah yana wa miyagu horo ta wajen sa su sha wahala?”

BABI NA 1

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? (Sashe na 2)

Zai yiwu mutum ya zama abokin Allah?

BABI NA 2

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah (Sashe na 1)

Mutane ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, to yaya za a ce ‘littafi ne daga Allah’?

BABI NA 2

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah (Sashe na 2)

Daya cikin abin da ke cikinsa da kila ya fi wasu sa mutane su tabbata cewa lallai Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne.

BABI NA 3

Mene Ne Nufin Allah Game da Duniya? (Sashe na 1)

Nufinsa ne abubuwa su kasance yadda suke a yanzu?

BABI NA 3

Menene Allah Ya Nufa ga Duniya?—(Sashe na 3)

Mene ne Allah zai yi don ya magance matsalolin wannan duniya?

BABI NA 4

Wane ne Yesu Kristi? (Sashe na 1)

Wace amsa ce za ka ba wa wanda ya ce Yesu mutumin kirki ne kawai?

BABI NA 4

Wane ne Yesu Kristi? (Shashe na 2)

Ta yaya za ka amsa ma wani da ya gaskata cewa Yesu, Allah ne?

BABI NA 4

Wane ne Yesu Kristi? (Sashe na 3)

Ta yaya ya nuna yana da kwazo da kuma hikima?

BABI NA 5

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah (Sashe na 1)

Shin hakkinmu ne mu sami fansa domin muna yin ayyuka masu kyau?

BABI NA 6

Ina Matattu Suke? (Sashe na 1)

Shin suna rayuwa ne a wani wuri dabam? Suna cikin hell ne?

BABI NA 7

Bege na Gaskiya ga Kaunatattunka da Suka Mutu (Sashe na 1)

Idan yi kuka yayin da aka maka mutuwa, hakan ya nuna ba ka ba da gaskiya da tashin matattu ba ne?

BABI NA 7

Bege na Gaskiya ga Kaunatattunka da Suka Mutu (Sashe na 2)

Me za ka ce idan wani ya ce batun tashin matattu ba gaskiya ba ne?

BABI NA 8

Mene ne Mulkin Allah? (Sashe na 1)

Me ya sa Allah ya ba wa ’yan Adam damar yin sarauta a sama tun da akwai mala’iku da yawa da za su iya yin hakan?

BABI NA 8

Mene Ne Mulkin Allah? (Sashe na 2)

Mene ne Mulkin ya riga ya cim ma? Mene ne zai cim ma a nan gaba?

BABI NA 9

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na Karshe”? (Sashe na 1)

Wasu ba su yarda cewa muna rayuwa a kwanaki na karshe ba. Me ya sa ka tabbata cewa muna gab da karshen wannan zamanin?

BABI NA 10

Bauta da Allah Ya Amince da Ita (Sashe na 2)

Gaskata cewa Allah yana wanzuwa shi ne kadai abin da ake bukata mu yi? Ko dai akwai abin da yake bukatar masu bauta masa su yi ban da wannan?

BABI NA 10

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu (Sashe na 2)

Laifi ne mutum ya so ya san sihiri?

BABI NA 11

Me Ya Sa Allah Ya Kyale Mutane Su Sha Wahala? (Sashe Na 1)

Idan Allah ne mai iko duka, hakan yana nufin cewa shi ne yake haddasa duka mugayen abubuwan da suke faruwa?

BABI NA 11

Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala? (Sashe na 2)

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa ga wannan tambayar mai wuya.

BABI NA 12

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai (Sashe na 1)

Shin za ka iya zama aminin Allah? Ka bincika abin da ka yi imani da shi kuma me ya sa ka yi imani da hakan? Mene ne Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

BABI NA 12

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai (Sashe na 2)

Za mu iya faranta wa Allah rai ko da Shaidan yana kokarin jawo mana masifu?

BABI NA 12

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai (Sashe na 3)

Sai ka yi kokari sosai kafin ka iya bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Idan ka yi hakan, me za ka samu?

BABI NA 13

Ra’ayin Allah Game da Rai (Sashe na 1)

Rai kyauta ce daga Allah. Ta yaya yadda muke bi da rayuwarmu da kuma na wasu zai nuna cewa muna daraja rai? Mene ne ra’ayin Allah game da zubar da ciki da kuma kisa?

BABI NA 13

Ra’ayin Allah Game da Rai (sashe na 2)

Wannan umurni don nazari zai taimaka maka ka bincika abin da ka yi imani da shi game da kara jini a jiki kuma zai taimaka maka ka iya bayyana ma wasu abin da ka yi imani da shi.

BABI NA 14

Yadda Za Ka Sa Iyalinka ta Yi Farin Ciki (Sashe na 2)

Ta yaya iyaye da yara za su amfana daga misalin Yesu? Ka bincika abin da ka yi imani da shi, da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.

BABI NA 15

Bauta da Allah Ya Amince da Ita (Sashe na 1)

Shin, Allah ya amince da dukan addinai? Idan ba haka ba, ta yaya za mu iya sanin addini na gaskiya? Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun kuma ka bincika abin da ka yi imani da shi.

BABI NA 15

Bauta da Allah Ya Amince da Ita (Sashe na 2)

Gaskata cewa Allah yana wanzuwa shi ne kadai abin da ake bukata mu yi? Ko dai akwai abin da yake bukatar masu bauta masa su yi ban da wannan?

BABI NA 16

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya (sashe na 1)

Shin Allah yana so mu rika yin da bukukuwan ranar haihuwa da ranakun hutu na addinai da kuma amfani da sifofi a bautarmu? Wadanne ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne za mu iya amfani da su?

BABI NA 17

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a (Sashe na 1)

Ta yaya za ka iya zama abokin Allah? Ta yaya za ka san cewa Allah yana sauraron addu’o’inka?

BABI NA 17

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a (Sashe na 3)

Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah yana amsa addu’o’in a hanyoyi dabam dabam. Ta yaya Jehobah zai amsa addu’o’inka ko a wane lokaci?

BABI NA18

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah (Sashe na 1)

Me ya sa wajibi ne mutum ya yi baftisma kafin ya zama Kirista? Mene ne zai iya sa Kirista ya yi baftisma?

BABI NA18

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah (Sashe na 2)

Kafin mutum ya yi alkawari cewa zai bauta wa Allah, wadanne matakai ne ya kamata ya dauka? Ta yaya ɗaukan alkawarin bauta wa Allah yake iya shafan rayuwar mutum da kuma makasudansa a nan gaba?

BABI NA18

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah (Sashe na 3)

Me ake bukata daga wurin mutumin da ya yi alkawarin bauta wa Allah? Me ya sa Kiristocin da suke kaunar Allah za su iya tabbata hakan ta wurin cika alkawarinsu na bauta wa Allah da dukan zuciyarsu?

BABI NA 19

Ka Tsare Kanka Cikin Kaunar Allah (Sashe na 1)

Ta yaya za ka iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah? Shafin nan zai taimaka maka ka bincika abin da ka yi imani da shi da kuma yadda za iya bayyana wa wasu.

BABI NA 19

Ka Tsare Kanka Cikin Kaunar Allah (Sashe na 2)

Me zai taimaka maka ka ci gaba da kusantar Allah bayan ka koyi gaskiya game da shi?