Koma ka ga abin da ke ciki

Tambayoyin da Matasa Suke Yi—Amsoshin da Suka Dace, Littafi na 1

Tambayoyin da Matasa Suke Yi—Amsoshin da Suka Dace, Littafi na 1

‘Ta yaya zan iya yin taɗi da iyayena?’ Ta yaya zan iya samun abokai?’ ‘Akwai laifi ne a yin jima’i na ɗan lokaci?’ ‘Me ya sa nake yawan fushi haka?’

Idan ka taɓa tambayar kanka irin wannan tambayar, to ba kai kaɗai ba ne. Ya dangana ga inda ka ke nemar amsar, ƙila ka gamu da amsoshin da suka sha bambam. Tambayoyin Da Matasa Suke Yi—Amsoshin da Suka Dace, Littafi na 1 (Turanci) zai taimake ka. Shawarsa yana bisa ƙa’idodi ne masu amfani daga cikin Littafi Mai Tsarki. Kalmar Allah ta taimake miliyoyin mutane su sha kan matsalolin da ake fuskanta cikin rayuwa. Ka bincika yadda zai iya taimake ka!

Wannan littafin yana ɗauke da waɗannan batutuwa:

  • Yadda za ka bi da Iyali

  • Wanene Kai

  • Cikin Aji da Kuma Waje

  • Jima’i, Ɗabi’o’i, da Kuma Soyayya

  • Munanan Halaye

  • Lokacinka na Shaƙatawa

  • Bautarka

  • Rataye Domin Iyaye

Za ka iya sauko da littafin daga tsarin PDF, ko kuma kana iya yin odar littafin ta wurin rubuta wa ofishinmu.