Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Idan Bala’i Ya Fado Mini?

Me Zan Yi Idan Bala’i Ya Fado Mini?

 Bala’i zai iya shafan kowa, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ba kullum maguji ke cin tsere ba, ba kullum jarumi ke cin nasara ba, ... amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.’ (Mai-Wa’azi 9:11, Littafi Mai Tsarki) Hakan yana shafan matasa ma. Ta yaya wasu matasa suka magance wannan matsalar? Ka yi la’akari da misalai biyu.

 REBEKAH

 Iyayena sun kashe aure sa’ad da nake shekara 14.

 Na gaya wa kaina cewa iyayena ba su kashe aurensu ba, babana yana bukatar lokaci ne kawai ya huce. Don me zai kashe aurensa da mamata bayan yana sonta? Me ya sa ya watsar da ni?

 Na kasa gaya wa mutane abin da ke faruwa, domin na so in mance da batun gaba daya. Na yi fushi sosai ko da yake a lokacin ban fahimci cewa ina fushi ba. Na damu sosai, har ba na iya barci.

 Sa’ad da na kai shekara 19, mahaifiyata ta rasu. Ita ce babbar kawata.

 Yadda iyayena suka kashe aure ya sa ni bakin ciki sosai, amma rasuwar mahaifiyata ya jefa ni cikin wani mummunar yanayi fiye da kashe auren da suka yi. Har yanzu bai fita daga zuciyata ba. Yanzu na ma kasa barci fiye da dā kuma ina kan damuwa har wa yau.

 Duk da haka, na sami taimako. Alal misali, Misalai 18:1 ta ce kada mu ware kanmu, kuma ina kokari in bi wannan shawarar.

 Kari ga haka, ina kokarin karanta littattafanmu masu ban karfafa, da yake ni Mashaidiyar Jehobah ce. Wani littafin da ya taimake ni sa’ad da iyayena suka kashe aure shi ne Questions Young People Ask—Answers That Work. Na tuna cewa na karanta wani babi a kundi na 2 mai jigo “Can I Be Happy in a Single-Parent Family?” (Zan Iya Jin Dadin Zama da Mahaifina ko Mahaifiyata Idan Suka Rabu?)

 Daya daga cikin nassosin da suke taimaka mini in kwantar da hankalina shi ne, Matta 6:25-34. A aya ta 27, Yesu ya yi wannan tambaya: “Wane ne fa daga cikinku, bisa ga alhininsa, yana da iko ya kara ko kamu * daya ga tsawonsa?”

 Munanan abubuwa za su faru da dukanmu, amma na koya daga wurin mahaifiyata cewa yadda muke bi da munanan yanayi yana iya taimakawa. Ta fuskanci matsaloli da yawa, rabuwa da mijinta da kuma ciwo marar magani, amma duk da haka, ta kasance da ra’ayi mai kyau kuma ta rike imaninta har mutuwarta. Ba zan taba mantawa da abubuwan da ta koya mini game da Jehobah ba.

 Ga abin bimbini: Ta yaya karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka ka jure matsaloli?​—Zabura 94:19.

 CORDELL

 Ina kallo sa’ad da mahaifina ya rasu a lokacin da nake dan shekara 17. Rasuwarsa ce abu mafi zafi da ya taba faruwa da ni. Na rikice gaba daya.

 A zuciyata, na dauka cewa bai mutu ba tukun, na kasa yarda cewa shi ne aka lulluba da zani. Na gaya wa kaina, ‘Zai tashi gobe.’ Na yi bakin ciki kwarai kuma na rikice gaba daya.

 Dukanmu a iyalinmu Shaidun Jehobah ne, kuma ikilisiyarmu ta taimaka mana sosai a lokacin da mahaifinmu ya rasu. Sun ba mu abinci, sun zauna da mu kuma sun tabbata cewa a duk lokacin da muke bukatarsu suna nan. A ra’ayina, yadda suka taimake mu ya nuna cewa Shaidun Jehobah ne Kiristoci na gaskiya.—Yohanna 13:35.

 Nassin da ya taimaka mini sosai shi ne 2 Korintiyawa 4:17, 18. Wurin ya ce: “Don wannan ’yar wahala tamu mai saurin wucewa ita ke tanadar mana madawwamiyar daukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido ke gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.”

 Aya ta karshe ce ta fi taimaka min. Mahaifina ya sha wahala na lokaci kadan kawai, amma abin da Allah ya yi alkawari zai faru a nan gaba zai dawwama har abada. Mutuwar mahaifina ya ba ni damar yin tunani a kan yadda nake rayuwa kuma na daidaita makasudaina.

 Ga abin bimbini: Ta yaya wani bala’i da ya auku a rayuwarka zai iya taimaka maka ka daidaita makasudinka a rayuwa?​—1 Yohanna 2:17.

^ Tsawon kamu ya yi daidai da santimita 45, ko kuma kafa daya da rabi.