Ga yadda za ka iya bi da yanayin.

Ka fadi gaskiya. Idan ba ka yi haka ba, iyayenka ba za su kara amince da kai ba. Saboda haka, ka fadi gaskiya kuma ka bayyana yanayin dalla-dalla.​—Misalai 28:13.

  • Ka guji neman hujja ko kuma mai da abin wasa.

  • Ko da yaushe ka tuna cewa “Mayar da magana da taushi ya kan juyar da hasala.”​—Misalai 15:1.

Ka ba da hakuri. Idan ka ba da hakuri don damuwa ko bakin ciki ko kuma karin aiki da ka jawo, hakan zai iya sa a sassauta maka. Duk da haka, ya kamata ka nuna cewa ba ka ji dadin abin ka yi ba kwarai.

Ka dauki nauyin abin da ka aikata. Idan ka dauki nauyin abin da ka yi, hakan zai nuna cewa ka manyanta. Kila abin da ya kamata ka yi shi ne ka yi iya kokarinka don iyayenka su sake yarda ka kai.—Misalai 20:11.

Ka tuna cewa iyayenka suna da ikon hana ka yin wasu abubuwan da za ka so yi. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “umurnin ubanka” da kuma “dokar uwarka.”​—Misalai 6:​20.

Idan kana son iyayenka su kara ba ka ’yanci

  • Ka nuna musu cewa kana son bin dokokinsu.

  • Ka yi kokarin sa biyayya ta zama halin da aka san ka da ita.