Littafi Mai Tsarki ya ce ‘watsa jiki tana da amfani.’ (1 Timotawus 4:8) Duk da haka, matasa da yawa da suke cewa “Ina bukata na rika motsa jiki” suna jinkirin yin haka.

  • Richard, dan shekara 21 ya ce: “Sa’ad da nake makaranta, abin mamaki matasa sukan fadi jarabawar motsa jiki. Alhali wannan jarabawar ita ce mafi sauki, kamar cin tuwo.”

  • Ruth ’yar shekara 22 ta ce: “Wasu suna tunani cewa ‘Mene ne amfanin gudu a cikin rana har sai ka yi zufa kuma ka gaji bayan za ka iya wasan bidiyo da zai nuna hoton wani da ke yin haka?’ ”

Idan haka ne kake ji, ka yi la’akari da fa’idodi uku da ake samu daga tsarin motsa jiki a kai a kai.

Fa’ida ta 1. Motsa jiki zai inganta garkuwar jikinka. Rachel, ’yar shekara 19 ta ce “Mahaifina yakan gaya mana cewa ‘Idan ba ka da lokacin motsa jiki, gara ka yi shirin rashin lafiya.’ ”

Fa’ida ta 2. Motsa jiki zai sa ka natsuwa. Emily, ’yar shekara 16 ta ce, “Sa’ad da nake tunani sosai, yin gudu yana taimaka mini don jikina zai wartsake kuma hankalina ya kwanta.

Fa’ida ta 3. Motsa jiki zai iya sa ka dada annashuwa. Ruth ta ce, “Ina sha’awar wasannin waje. Wadannan wasannin sun hada da hawan duwatsu, iyo, da kuma tukin keke.

Abin da zai sa ka yi nasara: Ka kebe akalla minti 20 sau uku kowane mako don yin wasan motsa jiki da kake jin dadinsa.

Ka tuna wannan: Ko da yake kwayoyin halitta suna da alaka da yanayin jikin mutum, amma yawanci, salon rayuwarka ne ya fi shafan lafiyar jikinka. Saboda da haka, sa’ad da ka ce “Ina bukata na rika motsa jiki,” kada ka manta cewa za ka iya daukan matakin!