Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Don In Rage Jin Kunya?

Me Zan Yi Don In Rage Jin Kunya?

 Matsalar: Jin kunya zai iya hana ka yin abokai da kuma wasu abubuwa da za su sa ka ji dadin rayuwa.

 Albishirin: Jin kunya zai iya amfanar mutum. Zai iya sa ka yi tunani kafin ka yi magana kuma ya sa ka rika saurarar mutane da kyau.

 Karin albishiri: Idan kai mai kunya ne yanzu, hakan ba ya nufin cewa za ka zama mai kunya a duk rayuwarka. Za ka iya shawo kan kunya, kuma wannan talifin zai bayyana yadda za ka yi hakan.

 Ka san abin da ke ba ka tsoro

 Kunya za ta iya sa ka ji tsoron yin magana da mutane ido-da-ido. Amma idan ka bincika kuma ka gane abubuwan da suke sa ka jin tsoro, kila ka ga cewa ba su taka kara sun karya ba. Ga wasu misalai guda uku.

 •   Abu na 1 da ke sa tsoro: “Ba ni da abin da zan yi tadi a kai da wani.”

   Gaskiyar batun: Halin da ka nuna sa’ad da kake tare da mutane ne za su fi tunawa, ba abin da ka fada ba. Za ka iya rage jin tsoro idan ka kasa kunne da kyau sa’ad da mutane suke magana.

   Ka yi tunani a kan wannan: Wane irin aboki ka fi so, wanda ya cika surutu ne ko wanda yake sauraron ka idan kana magana?

 •   Abu na 2 da ke sa tsoro: “Za a ce ni ban iya yin ma’amala da mutane ba.”

   Gaskiyar batun: Dole mutane su fadi ra’ayinsu game da kai, ko da kai mai kunya ne ko a’a. Za ka iya shawo kan tsoron da kake ji ta wurin yin tadi da mutane, don hakan zai sa su san ko kai wane irin mutum ne.

   Ka yi tunani a kan wannan: Idan kana tsammanin cewa kowa yana shari’anta ka, anya, ba kai ne kake shari’anta su domin ka dauka cewa ba sa son ka ba?

 •   Abu na 3 da ke sa tsoro: “Zan ji kunya idan na fadi abin da ba daidai ba.”

   Gaskiyar batun: Hakan na faruwa da kowa. Za ka iya shawo kan tsoron da kake ji ta wajen mai da abin da ka fada wasa idan ka yi kuskure.

   Ka yi tunani a kan wannan: Ya kake ji idan kana tare da mutanen da suke yarda cewa su ma sukan yi kuskure?

 Ka sani? Wasu mutane suna ganin su ba masu jin kunya ba ne domin sun saba tura sako ta waya. Amma zai fi sauki ka sami abokan kirki idan kana magana da mutane ido-da-ido. Wata mai suna Sherry Turkle da ta kware a fannin fasaha da ilimin halin dan Adam ta rubuta cewa: “Idan muna ganin juna ido-da-ido kuma muna jin muryar juna ne za mu dada kusantar juna.” *

Idan ka shawo kan abin da ke sa ka jin tsoro, za ka ga cewa yin magana da mutane ido-da-ido bai da wuya

 Abubuwan da za ka yi

 •   Kada ka gwada kanka da wani. Ba sai ka canja ka zama mai surutu ba. Abin da ya kamata ka yi shi ne ka rage jin kunya domin ka samu ka yi abokan kirki kuma ka ji dadin wasu abubuwa a rayuwa.

   Wata mai suna Alicia ta ce: “Ba sai ka dade kana magana da mutane ko ka zama wanda yake jan hankalin kowa ba. Ka dai gabatar da kanka ga wani da ba ka sani ba, ko ka yi masa wasu kananan tambayoyin kawai.”

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Bari kowa ya gwada aikinsa ya gani. Idan ya yi kyau, sa’an nan zai iya takama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.”​—⁠Galatiyawa 6:⁠4.

 •   Ka lura da abin da ke faruwa. Ka mai da hankali ga mutanen da ba sa jin kunya don ka ga yadda suke ma’amala da mutane. Me ke taimaka musu? Me ke taka musu birki? Wadanne halaye masu kyau ne suke da su da za ka so ka koya?

   Wani mai suna Aaron ya ce: “Ka lura da abin da mutanen da suke kulla abota da wuri suke yi, kuma ka yi koyi da su. Ka yi la’akari da abin da suke yi da abin da suke fada sa’ad da suka hadu da mutum a karo na farko.”

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kamar yadda karfe da karfe sukan wāsa juna, haka mutum da mutum sukan gyara rayuwar juna.”​—⁠Karin Magana 27:⁠17.

 •   Ka rika yin tambayoyi. Mutane sukan so su fadi ra’ayinsu, don haka idan ka yi musu tambayoyi, zai yi sauki ka soma tattaunawa da su. Kuma zai sa ba za a sa maka ido ba.

   Wata mai suna Alana ta ce: “Shirya abin da za ka yi tun da wuri zai sa ka rage jin tsoro. Za ka iya shirya wasu abubuwa da za ka fada ko tambayoyin da za ka yi kafin ka je wani liyafa da ka san za ka hadu da sabbin mutane.”

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ku kula da kanku kadai, amma ku kula da wadansu kuma.”​—⁠Filibiyawa 2:⁠4.

^ From the book Reclaiming Conversation.