Koma ka ga abin da ke ciki

Ina Jin Kadaici

Ina Jin Kadaici

Abin da za ka iya yi

 1. Ka mai da hankalinka ga abin da za ka iya yi. (2 Korintiyawa 11:6) Ko da yake yana da kyau ka san kasawarka, har ila kana da halaye masu kyau. Sanin halaye masu kyau da kake da su zai ba ka gaba gadin da kake bukata don ka shawo kan jin kadaici. Ka yi tambayi kanka, ‘Wadanne halaye masu kyau nake da su?’ Ka yi tunanin a kan wasu abubuwan da ka iya ko kuma halayenka masu kyau.

 2. Ka so mutane sosai. Ka soma da mutane kadan. “Ta wurin gai da mutane ko kuma tambayar lafiyarsu da ayyukansu, za ka san su sosai,” in ji wani matashi mai suna Jorge.

Za ka iya kawar da abin da ke raba ka da tsaran ka

 Taimako: Kada ka yi abokantaka da tsararka kawai. Wasu daga cikin abota masu kyau da aka yi maganarsu a cikin Littafi Mai Tsarki tsakanin wadanda suka girmi juna sosai ne, kamar su Ruth da Naomi, Dauda da Jonathan, Timotawus da Bulus. (Ruth 1:16, 17; 1 Sama’ila 18:1; 1 Korintiyawa 4:17) Kuma ka tuna cewa ba mutum daya ne kawai ke mamaye yin tadi ba. Mutane sun fi son tadi masu sauraro sosai. Saboda haka, idan kana yawan jin kunya, ka tuna cewa—tadi za ka yi ba jawabi ba!

 3. Ka kasance da “juyayi.” (1 Bitrus 3:8) Ko da ba ka yarda da ra’ayin mutumin ba, ka hakura ka bar shi ya yi magana. Ka yi zance a kan abin da ra’ayinku ya za daya a kai. Idan ba ka yarda da wani batu ba, ka nuna hakan a hankali kuma cikin basira.

 Taimako: Ka yi magana da mutane yadda za ka so su yi da kai. Halin ka-ce na-ce ko na tsokana, zagi, ko kuma halin na-fi-kowa-kirki zai sa mutane su guje ka. Mutane za su fi son ka idan ‘zancenka kullum yana kasancewa da alheri.’—Kolosiyawa 4:6.