Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Shin Ya Kamata Na Sha Giya Ne?

Shin Ya Kamata Na Sha Giya Ne?

 Littafi Mai Tsarki bai haramta shan giya ba idan mutum ya kai ya sha. Amma, ya haramta yin maye da giya ko kuma buguwa.—Zabura 104:15; 1 Korintiyawa 6:10.

 Amma idan aka matsa maka ka sha giya kuma hakan zai sa ka taka dokar kasa da kuma wadda iyayenka suka kafa fa?

 Ka yi tunanin abin da zai iya faruwa

 Wasu cikin tsararka za su iya jin cewa shan giya abin da zai sa ka more rayuwarka ne. Amma, me zai iya faruwa bayan ka sha giyar?

  •  Za ka iya taka doka. Idan kana zama a kasar da gwamnati ta hana yara shan giya kuma idan ka sha, za a kama ka da yin laifi kuma ka biya tara ko a kwace lasisin ka na tuki ko a ce ka yi wani aiki wa jama’a ko kuma a jefa ka cikin kurkuku.​—Romawa 13:3.

  •  Zai iya bata maka suna. Idan mutum ya sha giya, yana iya yin abubuwan da ba su dace ba. Kuma in ya bugu, yakan yi maganar banza ko kuma ya aikata wani abin da daga baya zai yi da-na-sani. (Misalai 23:31-33) A zamanin nan da dandalin sada zumunta na intane ya zama ruwan dare, duk wani abin da mutum ya fada ko ya saka a shafin, zai iya bata sunansa kuma ba za a iya sharewa da sauki.

  •  Zai iya jefa ka cikin matsala. Buguwa da giya zai sa mutum ya fada cikin masifa, za a iya ma mutumin fyade. Kuma hakan zai iya sa mutum ya bi ra’ayin abokansa har ya kai ga taka doka ko fadawa cikin wani bala’i.

  •  Za ka iya zama mashayin giya. Wani bincike ya nuna cewa idan yaro ya soma shan giya tun yana karami, yana da sauki ya zama mashayin giya. Idan kana shan giya don ka rage damuwa ko don kadaici, hakan zai iya zama maka tarko kuma zai yi wuya ka daina shan giya kullum.

  •  Za ka iya mutuwa. A wata shekarar da ta shiga, wani rahoto ya nuna cewa sanadiyyar shan giya, mutum daya cikin hudu na mutuwa don hatsarin mota a cikin kowane minti 52 a Turai. Kuma an gano cewa kashi daya cikin hudu na matasa maza (masu shekaru tsakanin 15-29) ne ke mutuwa, sa’an nan daya cikin goma na matasa mata ne ke mutuwa sanadiyyar shan giya a Turai. Idan kai ba ka sha giya amma ka shiga motar wanda ya yi tilis da giya, kana sa ranka cikin hadari.

 Ka dauki mataki

 Za ka iya ka guje wa mummunar sakamakon da shan giya zai iya haifarwa idan ka dauki mataki tun da wuri.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya.” (Misalai 22:3) Bai kamata mutum ya sha giya kafin ya yi tuki ko kuma wani abin da yake bukatar natsuwa ba.

 Abin da zan yi: ‘Zan jira sai na mallaki hankalina kuma a lokacin da ya dace kafin in soma sha giya.’

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya.” (Romawa 6:16, Littafi Mai Tsarki.) Idan kana shan giya domin tsararka suna sha, hakan ya nuna cewa ba za ka iya tsai da shawara da kanka ba. Idan damuwa ko kadaici ne ya sa ka ka shiga shan giya, hakan ya nuna cewa kana bukatar ka koya yadda za ka bi da matsalolinka.

 Abin da zan yi: ‘Ba zan yarda tsara na su sa ni shan giya ba.’

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka kasance kana cikin masu shaye-shaye.” (Misalai 23:20) Tarayya da abokan banza zai hana ka cim ma burinka. Za ka iya soma shan giya idan kana tarayya da mutanen da suke yawan shan giya.

 Abin da zan yi: ‘Ba zan zama abokin wadanda suke yawan shan giya ba.’