Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Kamata in Sani Game da Wasannin Bidiyo?

Me Ya Kamata in Sani Game da Wasannin Bidiyo?

 Wasan watsa kwakwalwa na wasannin bidiyo

 A kasar Amirka, inda wasannin bidiyo kasuwanci ne mai kawo riba sosai . . .

 1.   Mene ne yawan shekarun wadanda suke wasannin bidiyon?

  1.   18

  2.   30

 2.   Maza nawa ne kuma mata nawa ne ke yin wasan bidiyon?

  1.   Maza kashi 55 bisa dari; mata kashi 45 bisa dari

  2.   maza kashi 15 bisa dari; mata 85 bisa dari

 3.   A cikin rukunin nan biyu, su wa suka fi yawa a yin wasan?

  1.   Mata daga shekara 18 ko sama da haka

  2.   Maza shekara 17 ko kasa da haka

 Amsoshi (daga kirgen 2013):

 1.   B. 30.

 2.   A. Matan sun kai kashi 45 bisa dari​—kusan rabin ’yan wasan.

 3.   A. Mata masu shekara 18 ko sama da haka sun kai kashi 31 bisa dari na masu yin wasan, sa’an nan maza masu shekara 17 ko kasa da haka sun kai kashi 19 bisa dari.

 Kirgen nan za su taimaka maka ka san wadanda suke yin wasannin. Amma ba za su gaya maka sakamakonsa ba, wato ko wasannin za su jawo mummunan sakamako ko sakamako mai kyau ba.

 Amfaninsa

 Wanne ne cikin wadannan furuci game da wasannin bidiyo ka yi na’am da shi?

 •  Irene ta ce: “Hanyoyin shakatawa ne tare da iyalai da kuma abokai.”

 •  Annette ta ce: “Suna taimaka wa mutum ya mance da matsalolinsa.”

 •  Christopher ya ce: “Suna taimaka wa mutum ya hanzarta yadda yake daukan mataki.”

 •  Amy ta ce: “Za su taimake ka ka inganta sanin yadda za ka magance matsaloli.”

 •  Anthony ya ce: “Suna sa mutum ya wasa kwakwalwarsa, wato suna sa mutum ya zama mai tunani, mai tsari da kuma mai dabara.”

 •  Thomas ya ce: “Wasu wasannin suna karfafa yin abu tare da abokai.”

 •  Jael ta ce: “Wasu wasannin suna taimaka wa mutum ya gyara siffarsa.”

 Shin ka yi na’am da wasu ne cikin wadannan kalaman nan ko kuma dukansu? Wasannin bidiyo za su iya amfanar hankalinka kuma su amfane ka a zahiri. Ko da cewa ana yin wasu wasannin ne don a ci lokaci ko kuma ya sa mutum ya “mance da matsalolinsa” ne kawai kamar yadda Annette ta ce, hakan ba laifi ba ne.

 ● Littafi Mai Tsarki ya ce “akwai lokacin yin kowane abu a duniya,” har da shakatawa ma.—Mai-Wa’azi 3:1-4.

 Muninsa

 Shin yin wasannin bidiyo suna cin lokacinka sosai?

 Annette ta ce: “Da zarar na soma yin wasannin, da kyar ne nake dasa aya. Zan yi ta ce wa kaina, ‘sauran hawa daya kawai!’ Kafin na ankara, na bad da sa’o’i da yawa ko ina yin wasannin!”

 Serena ta ce: “Wasannin bidiyo za su iya cinye lokaci sosai. Za ka bad da sa’o’i da yawa kana yi don ka dauka cewa kana yin wani abin kirki bayan da ka yi nasara a wasanni guda biyar, amma gaskiyar ita ce ba ka yi wani abin kirki ba.”

 Gaskiyar al’amarin: Idan ka yi hasarar kudi, za ka iya samun wani kudi. Amma idan ka bad da lokaci, ba za ka iya samunsa kuma ba. A takaice, lokaci ya fi kudi tamani. Kada ka yarda ka bad da shi!

 ● Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi tafiya cikin hikima . . . , kuna rifta zarafi.”—Kolosiyawa 4:5.

 Shin wasannin bidiyo suna shafan tunaninka?

 Seth ya ce: “Ana ‘yin’ laifuffuka da za su iya sa a jefa mutum a kurkuku ko kuma a kashe shi a wasannin bidiyo ba tare da yin tunani ba.”

 Annette ta ce: “Wasannin bidiyo da yawa sun kunshe yin nasara bisa magabtanka don ka cim ma burinka. Sau da yawa, hakan na nufin za ka kakkashe su.”

 Nathan ya ce: “Za ka yi mamakin wasu abubuwa da za ka rika gaya wa abokanka a wasu lokuttan yayin da kake yin wasannin. Alal misali, kalamai kamar ‘Ka Mutu’ ko kuma ‘Zan kashe ka!’”

 Gaskiya al’amarin: Ka guje wa wasannin da ke daukaka abubuwan da Allah ya haramta. Abubuwa kamar nuna karfi da lalata da kuma sihiri.—Galatiyawa 5:19-21; Afisawa 5:10; 1 Yohanna 2:15, 16.

 ● Littafi Mai Tsarki ya ce: Jehobah ya ki “mai-mugunta da mai-son zalunci.” (Zabura 11:5) Ko idan wasannin bidiyon da ka zaba ba su nuna irin mutumin da ka ke ba, zai iya nuna halinka.

 Abin lura: Littafin nan Getting to Calm ya ce: “Wasannin bidiyo masu nuna karfi suna shafan halin mutum sosai fiye da yadda telebijin ke yi, domin yaran ba sa kallon mugun bugun da ake yi cikin wasan kawai da mai neman nasara ke yi ba, amma su ne masu neman nasarar. Domin wasa yana da abin da yake koyar da shi, suna kuwa koyar da nuna karfi.”​—Gwada da Ishaya 2:4.

 Gaskiyar al’amari

 Matasa da yawa suna kokari su daidaita a yadda suke amfani da wasannin bidiyo. Ka bincika wadannan misalai biyu.

 Joseph ya ce: “Dā ina wasanni bidiyo sosai har cikin dare, da jin cewa ba na bukatar barci mai yawa ba. Bari na lashe wasan.’ Amma yanzu na daidaita game da wasannin bidiyo ina yinsu yadda ya kamata. Ina daukansu wasannin da zan iya yi ne don na wartsake a wasu lokutta. Saboda haka dole mutum ya daidaita duk abin da yake yi.

 David ya ce: “Na rage lokacin da nake batarwa wajen wasannin bidiyo kuma na iya cim ma wasu abubuwa! Na iya samun cin gaba a hidimar da nake yi, ina iya taimaka wa wasu a ikilisiyarmu har ma ina koya buga kidi. Da akwai abin yi da yawa na wartsakewa.

 ● Littafi Mai Tsarki ya ce mutane da suka manyanta ‘masu-kamewa’ ne. (1 Timotawus 3:2, 11) Suna more nishadi da suke yi domin sun san lokacin da ya kamata su daina kuma kame kansu game da hakan.—Afisawa 5:10.

 Batun shi ne: Yin wasan bidiyo nishadi na za a iya more shi daidai. Amma kada ka yarda wasannin ya sarrafa rayuwarka da ba za ka iya yin wasu muhimman abubuwa ba. Hakika, maimakon mu yi ta kokarin neman lashe wasa, ba zai fi kyau mu yi amfani da wannan lokaci mu iya cim ma wani abin da zai kai mu samun rayuwa mai kyau ta nan gaba ba?