Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Sami Isashen Barci?

Ta Yaya Zan Sami Isashen Barci?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma hannu daya cike, tare da kwanciyar rai, da hannu biyu cike, tare da wahala da cin iska kawai.” (Mai-Wa’azi 4:6) Idan ba ka sami isashen barci ba, ba za ka iya yin aiki da kyau ba!

  • “Idan ban sami isashen barci ba, ba na iya tattara hankalina na yi abu da kyau!”—Rachel, 19.

  • “Da karfe 2:00 na rana ne, amma na gaji tilis har kamar barci zai kwashe a tsakiyar tadi!”—Kristine, ’yar shekara 19.

Kana bukatar isashen barci ne? Ga abin da wasu tsaranka suka yi.

Ka guji yin dare sosai. Ina kokarin soma kwanciya da wuri,” in ji Catherine, ’yar shekara 18.

Ka rage lokacin hira. Wasu lokuta abokai za su kira na a waya ko kuma su aika min sakon tes,” in ji Richard, dan shekara 21, “amma kwanan nan nakan katse tadin kuma na shiga barci.

Ka ayana lokacin barci da kuma farkawa. Jennifer ’yar shekara 20, ta ce: “Kwanan nan, ina kokarin soma barci da wuri kuma na farka a lokaci daya kowace rana.

Abin da zai ka yi nasara: Ka kokarta ka rika yin barcin akalla awa takwas kowane dare.

Kai ne za ka amfana idan ka dauki matakai da za su sa ka sami isashen barci. Ka tuna cewa kasancewa da koshin lafiya zai sa ka karfin jiki da annuri kuma zai sa ka rika hidimominka da kyau sosai.

Lafiyar jikinka ba kamar wasu abubuwa da ba ka da iko a kai ba don za ka iya daukan mataki a kai. Wata ’yar shekara 19 mai suna Erin ta ce, “Gaskiyar ita ce, za ka iya kasancewa da koshin lafiya kuma hakan ya dangana ne ga mutum daya, wato kai.