Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Kamata Na Sani Game da Aika Sako Ta Wayar Selula?

Me Ya Kamata Na Sani Game da Aika Sako Ta Wayar Selula?
  • :-) Aika sako hanyar sadarwa ce mai kyau idan aka yi amfani da fasalin yadda ya dace.

  • :-( Idan ba a yi amfani da fasalin bisa ka’ida ba, zai iya bata abota da suna.

Wannan talifin zai tattauna abin da ya kamata ka sani game da

Kari ga haka, talifin zai tattauna:

 Wanda kake aika wa sako

 Matasa da yawa sun dauki aika sako wata muhimmiyar hanyar sadarwa ce. Aika sako hanya ce ta sadarwa da dukan wadanda kake da lambarsu a wayarka​—sai dai idan iyayenka ba su yarda ba.

 “Babanmu ba ya so ni da kanwata mu rika tadi da samari. Idan ma ya yarda, za mu yi hakan ne a kan waya tarho da ke cikin falo kuma a idon wasu.”​—Lenore.

 Abin da ya kamata ka sani: Idan ka ba kowa lambarka, kana iya shiga masifa.

 “Idan ba ka mai da hankali ga wadanda kake ba wa lambarka ba, za a iya aika maka da sakonni ko hotuna da ba ka so.”​—Scott.

 “Idan kana aika sako wa yarinya koyaushe, hakan zai iya sa ku shaku da juna sosai ba tare da bata lokaci ba.”​—Steven.

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya buya.” (Misalai 22:3) Idan ka dauki wasu matakai, za ka iya guje wa masifa.

 Labari: “Ni da wani yaro abokai ne, kuma muna aika sako wa juna sosai. Na dauka mu abokai ne kawai. Ban yi tsammanin hakan na da hadari ba sai da ya gaya mini yana so na. Da na sani da ban yi abota da shi​—da kuma aika masa sakonni​—yadda na yi ba.”​—Melinda.

 Ka yi la’akari: Sa’ad da Melinda ta gane yadda yaron yake ji, yaya kake ganin hakan zai shafi abotarsu?

 Ka rubuta labarin a wata hanya dabam! Da a ce Melinda ta dauki wasu matakai da abotar ta da yaron ba zai wuce gona da iri ba. Wadanne matakai ke nan?

 Irin sakon da kake aikawa

 Aika da sakonni bai da wuya ​—kuma karanta sako abin marmari ne​—ana saurin manta cewa mutane za su iya fahimtar sako ta wata hanya dabam.

 Abin da ya kamata ka sani: Wani zai iya fahimtar sakon da ka aika ta wata hanya dabam.

 “Ba za ka iya fahimtar yadda mutumin yake ji ko muryarsa ba​—ko da ya yi amfani da alamu a cikin sakon. Kuma hakan zai iya jawo rashin fahimta”​—Briana.

 “Na san wasu ’yammata da suka zub da mutuncinsu kuma an dauke su masu kwarkwasa ne domin irin sakon da suke aika wa samari.”​—Laura.

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.” (Misalai 15:​28) Mene ne darasin? Ka sake karanta sakon da ka rubuta kafin ka aika!

 Lokacin da kake aika sako

 Idan ka mai da hankali, za ka iya tsara ka’idarka game da aika sako.

 Abin da ya kamata ka sani: Idan ba ka mai da hankali ga yadda kake aika sako ba, za ka mai da kanka marar hankali kuma abokai za su guje ka maimakon su kusace ka.

 “Aika sako babu ka’ida bai da wuya. Nakan aika sako a lokacin da nake tadi da wani.”​—Allison.

 “Hadari ne mutum ya rika aika sako a lokacin da yake tuka mota. Idan ba ka kalli gabanka ba kana iya yin hatsari.”​—Anne.

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Akwai lokaci kuma domin kowane abu a karkashin sama, . . . lokacin shuru da lokacin magana.” (Mai-Wa’azi 3:1, 7) Hakan ya shafi aika sako kamar yadda ya shafi yin magana!

 Shawara game da aika sako

Wanda kake aika wa sako

  •  ;-) Ka bi ka’idodin da iyayenka suka tsara.​—Kolosiyawa 3:20.

  •  ;-) Ba kowa ba ne za ka ba wa lambarka. Sa’ad da ka ki gaya wa mutane wani abin sirri​—kuma ka ki ba su lambar wayarka—kana nuna basira ne kuma hakan zai taimake idan ka manyanta.

  •  ;-) Bai dace ku saba da wani ta wajen aika sakon soyayya ba tare da niyar aure ba. Idan soyayya ta shiga, hakan zai jawo bakin ciki da tashin hankali.

 “Iyayena sun san cewa ina amfani da wayar selulata yadda ya kamata, saboda haka sun tabbata zan tsai da shawara mai kyau game da irin mutanen da zan ba su lambata.”​—Briana.

Irin sakon da kake aikawa

  •  ;-) Kafin ka fara aika sako, ka yi wa kanka tambaya, ‘Aika sako ne zai fi dacewa a wannan yanayin?’ Zai fi kyau a wani lokaci ka yi wa mutum waya ko kuma ka jira sai kun hadu ido da ido.

  •  ;-) Kada ka aika sako game da wani abin da ba za ka iya fada da baki ba. Sarah, wata ’yar shekara 23 ta ce: “Idan ba za ka fadi wani abu da baki ba, kada ka aika da shi ta sako.”

 “Idan wani ya aika maka da hotunan batsa, ka gaya wa iyayenka. Zai zama kariya ce gare ka kuma ya sa iyayenka su amince da kai.”​—Sirvan.

Lokacin da kake aika sako

  •  ;-) Ka yanke shawara game da lokatan da ba za ka yi amfani da wayarka ba. Wata yarinya Olivia ta ce: “Ba na rike wayata sa’ad da nake cin abinci ko kuma idan ina nazari.” “Nakan kashe wayata a lokacin taron Kirista don kada ta raba min hankali.”

  •  ;-) Ka yi tunanin yadda aika sako zai shafi wasu. (Filibbiyawa 2:4) Ba shi da kyau ka tsaya kana magana da mutum sa’an nan kuma kana kokarin aika sako.

 “Na tsai da shawara cewa ba zan taba aika sako ba idan ina tare da abokai sai ko ya zama dole. Kuma ba na ba da lambata wa wadanda ban waye su ba.”​—Janelly.