Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Na Isa Fita Zance Kuwa?

Na Isa Fita Zance Kuwa?

 Mene ne fita zance?

  •   Kana yawan fita yawo da wata. Wannan fita zance ne?

  •   Kana kud da kud da wata. Kuna aika wa juna sako ko kuma kuna magana a waya sau da yawa a rana. Wannan fita zance ne?

  •   Duk lokacin da ku ke tare da abokai sai ku ware kanku da ita. To, wannan fita zance ne?

 Hakika, amsa tambayar nan ta farko ba za ta zama matsala a gare ka ba. Amma, kila za ka yi jinkirin amsa tambaya ta biyu da uku. To, mene ne ainihi fita zance ke nufi?

 Hakika, fita zance yanayi ne da ka ke sha’awar wata kuma ita ma tana sha’awar ganinka ko yaushe.

 Tambayoyi ukun nan amsarsu e ce. Idan kana magana da wata a waya ko kuma a boye, kai da abokiyarka kuna son juna kuma kuna zance kullum, hakan fita zance ne.

 Me ake nufi a fita zance?

 Ya kamata a kasance da dalili mai kyau na fita zance, zai taimaki matashin da matashiyar su ga ko za su iya yin aure.

 Amma, wasu tsararka suna iya daukan fita zance abin wasa ne. Kila suna dai jin dadin kasance da wata kawai, ba da nufin su aure ta ba. Wasun su suna aza cewa sun cim ma wani abu ne ko kuma abin da za su burge mutane da shi ne.

 Amma irin dangantakar nan ba ta dadewa. Wata matashiya, Heather ta ce: “Matasa da yawa da suke irin wannan cudanyar sukan rabu bayan mako guda ko biyu. Suna ganin cudanyar soyayya abin da za a yi ne kawai na dan lokaci, irin wannan ra’ayin zai jawo kisan aure maimakon a jure da aure.”

 A bayyane yake cewa sa’ad da ka ke fita zance da wata yakan shafi tunanin da za ta yi. Saboda haka, ka tabbata nufinka mai kyau ne.—Luka 6:31.

Idan ka soma fita zance ba tare da nufin yin aure ba, to kana kama da yaron da ke wasa da sabon abin wasa, bayan haka kuma ya yar da shi

 Ka yi tunanin wannan: Za ka so wata ta yi wasa da hankalinka kamar kayan wasan yara, da za su so shi na dan lokaci bayan haka kuma su yi watsi da su? To, kada ka yi wa wata haka! Littafi Mai Tsarki ya ce kauna “ba ta rashin hankali.”—1 Korintiyawa 13:4, 5.

 Wata matashiya mai suna Chelsea ta ce: “Ina tunanin cewa fita zance ya kamata a ji dadinsa, amma bai kamata namijin yana daukansa da muhimmanci sa’an nan kuma ita tana wasa da cudanyar ba.”

  Taimako: Don ka yi shirin fita zance da kuma yin aure, karanta 2 Bitrus 1:5-7 ka duba wani hali da ka ke bukatarsa. A cikin wata guda ka ga ko ka fahimci wannan halin, kuma ko kana bukatar gyara.

 Na isa fita zance kuwa?

  •    Shekara nawa ne ya kamata matashi ya kai kafin ya soma fita zance?

  •    To, ka yi wa iyayenka tambayar nan ta baya.

 Mai yiwuwa amsarka ta bambanta da na iyayenka. Ko kuma ta su ta yi daidai da taka! Kila kai matashi ne da ke son ka manyanta kafin ka soma fita zance don ka iya sanin abokiyarka sosai.

 Abin da Danielle, mai shekara 17 ta yi ke nan. Ta ce: “Shekara biyu da ta shige, halayen da nake so wajen wanda zan aura sun bambanta da na yanzu. Hakika, har yanzu, ban tabbata zan yi zaben da ya dace ba. Sa’ad da na tabbata cewa na gyara halina, wato, nan da ’yan shekaru, sai in soma tunanin fita zance.”

 Da akwai wani dalili kuma da ya sa ya dace a dan jira. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furucin nan “wuce lokaci” don a kwatanta lokacin da son yin jima’i da soyayya ke tsanani wajen matasa. (1 Korintiyawa 7:36) Idan kana kud da kud da wata sa’ad da kake irin wannan yanayi zai zama da sauki ku fada cikin jarabar yin lalata.

 Kila tsararka ba za su ga muhimmancin yin haka ba. Wasun su da yawa suna son su dana yin jima’i ne kawai. Amma za ka iya, kuma ya kamata kada ka yi irin tunanin nan! (Romawa 12:2) Balle ma, Littafi Mai Tsarki ya ce mu “guji lalatar jima’i.” (1 Korintiyawa 6:18, juyin New International Version) Idan ka jira don ka wuce lokaci, ba za ka ‘cuci jikinka’ ba.—Mai-Wa’azi 11:10.

 Me ya sa ya kamata na manyanta kafin na fita zance?

 Idan ka matsu ka fita zance babu shiri, daidai yake da tilasta maka ka yi wata jarrabawa da ba ka san kome game da ita ba. Babu shakka zai yi wuya! Kana bukatar lokaci don ka yi nazari game da batun kuma ka fahimci matsalolin da ke kunshe cikinta.

 Abu daya ne da fita zance.

 Fita zance ba batun wasa ba ne. Saboda haka, kafin ka soma fita zance da wata, kana bukatar ka koyi wani batu na musamman, yadda za ka karfafa cudanyarku.

 Daga baya, idan ka sami wadda ta dace, za ka iya bi da irin dangantakar nan da kyau. Shi ya sa aure mai nasara zumuncin abokai biyu ne.

 Idan ka dan jira kafin ka soma fita zance ba zai hana ka more rayuwa ba. Hakika, za ka ma fi more “kuruciyarka.” (Mai-Wa’azi 11:9) Za ka sami lokaci mai yawa da za ka gyara halayenka, musamman ma dangantakarka da Allah.—Makoki 3:27.

 Kafin lokacin, ka ci gaba da more abokantakarka da kishiyar jinsi. Ta yaya za ka yi wannan da kyau? Ta wurin shakatawa tare da maza da mata da suka manyanta. Wata yarinya mai suna Tammy ta ce: “Wannan ya fi dadi. Ya fi kyau kana da abokai da yawa.” Monica ta yarda cewa: “Shakatawa tare da jama’a mataki ne da ya dace, domin za ka sadu kuma yi tarayya da mutane da suke da halaye dabam dabam.”

 Bai dace ka rika ware kanka da wata ba, don haka zai sa ku fada cikin jaraba nan da nan. Saboda haka kada ka yi hanzari. Ka yi amfani da wannan lokaci a rayuwarka don ka samo kuma ka adana abokantakarka da mutane. Nan gaba, sa’ad da ka tsai da shawarar ka soma fita zance, zai zama ka shirya kuma za ka san abin da kake bukata wajen abokiyar rayuwarka.