Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Idan An Matsa Mini In Yi Jima’i Fa?

Idan An Matsa Mini In Yi Jima’i Fa?

Kana iya cewa, “ba gwamma na yi ba?” “Ballantana ma, kowa yana yi.”

Dakata ka yi tunani!

Gaskiyar: Ba kowa ba ne yake yi.

Hakika, kila ka karanta game da yawan mutanen da suke yi. Alal misali, wani bincike da aka yi a Amirka ya nuna cewa a lokacin da matasa suka gama makarantar sakandare, matasa 2 cikin 3 a kasar sun riga sun yi nisa wajen yin jima’i. Amma kuma hakan yana nufin cewa 1 cikin 3—ba sa yin haka kuma wannan adadi ne mai yawa.

Wadanda suke yi fa? Masu bincike sun gano cewa yawancin irin matasan nan suna fuskantar irin wadannan halaye.

Bakin ciki. Yawancin matasa da suka yi jima’i kafin aure sun ce sun yi da-na-sani daga baya.

Yin jima’i kafin aure yana kama ne da yin amfani da kyakkyawan hoto a matsayin tabarmar share kafa

Rashin Aminci. Bayan sun yi jima’in, su biyun za su soma tunani, ‘to wa ya sani ko da wa kuma ya ko ta taba yin jima’i?’

Bacin rai. A cikin zukatansu, ’yammata da yawa sun fi son wanda zai kāre su, ba wanda zai yi lalata da su ba. Kuma samari da yawa ba sa son yarinyar da suka riga suka kwana da ita.

Gaskiyar Al’amari: Jikinki da mutunci yake, kada ki zub da mutuncinki ta wajen bayar da jikinki. Ki nuna cewa kina da dabi’a sosai ta bin dokokin Allah game da guje wa yin jima’i kafin aure. Ranar da ki ka yi aure za ki iya yin jima’i. Kuma a lokacin za ki more shi sosai—ba tare da wani damuwa, bacin rai, da kuma rashin amincewa da ke tattare da yin jima’i kafin aure ba.—Misalai 7:22, 23; 1 Korintiyawa 7:3.