Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Malami na Ya Ki Jinina

Malami na Ya Ki Jinina

Dakata ka yi tunani!

Ka yi la’akari da abin da ya faru da Rachel. Rachel tana cin jarrabawar ta a makaranta sosai. Amma sa’ad da ta kai aji 7 sai lale ya canza. “Malamina ya yi iyakacin kokarinsa don na fadi jarabawarsa,” in ji Rachel. Mece ce damuwar? A bayyane yake cewa Malamin ba ya son addinin da Rachel da mahaifiyarta suke bi.

Kamar duwatsun da idan ka bi kansu za su taimake ka ka haye ruwa, haka ma idan ka bi da malamanka yadda ya dace za su taimake ka ka sami ilimi sosai

Me ya faru? Rachel ta ce: “A duk lokacin da malamin ya rage mini maki domin ya ki jinina, mahaifiyata takan biyo ni don ta tattauna zancen da shi. A karshe dai, ya daina matsa min.

Idan kana fuskantar irin wannan kalubalen, ka yi karfin zuciya ka gaya wa iyayenka. Babu shakka, za su so su yi magana da malamin kila ma har da hukumar makarantar don su magance yanayin.

A gaskiya, ba dukan matsaloli ne ake iya magancewa ba. A wasu lokuta, jimrewa kawai za ka yi. (Romawa 12:17, 18) “Daya daga cikin malamai na ba ya son dalibansa sam,” in ji Tanya. “Yana yawan zaginmu, yana cewa mu wawaye ne. Da farko, abin yakan sa ni kuka, amma daga baya sai na banza da zaginsa. Na mai da hankali ga aikina a duk lokacin da yake ajinmu, na yi kokarta sosai. Da haka, ba ya damu na kuma, kuma ina daya daga cikin wadanda suka ci jarabawarsa. Bayan shekara biyu, sai aka kori malamin.

Gaskiyar al’amarin shi ne: Ka san yadda za ka bi da malami mai wuyan hali kuma hakan zai amfane ka sosai a rayuwa, sa’ad da ka hadu da shugaba mai wuyan hali, za ka san yadda za ka bi da shi. (1 Bitrus 2:18) Za ka kuma san yadda za ka daraja nagargarun malamai sa’ad da ka hadu da su.