Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Idan Iyayena Ba Su da Lafiya?

Me Zan Yi Idan Iyayena Ba Su da Lafiya?

 Yawancin lokaci matasa ba su da marasa lafiya da suke bukatar su kula da su, domin mai yiwuwa sai bayan shekaru da yawa kafin iyayensu su yi rashin lafiya.

 Amma, idan mahaifinka ko mahaifiyarka ta soma rashin lafiya tun kana yaro fa? Ga labarin matasa biyu da suka fuskanci irin wannan yanayi mai wuya.

 Labarin Emmaline

 Mahaifiyata tana da cutar Ehlers-Danlos syndrome (EDS), wani irin cuta mai tsanani da ke shafan gabubuwanta da fatan jikinta da kuma jijjiyoyinta.

 Cutar ba ta da magani, kuma a cikin shekaru goma da suka shige yanayin mahaifiyata ya dada muni. A wasu lokatai, takan yi karancin jini har kamar ba za ta rayu ba ko kuma jikinta ya yi ta mata zafi har ta ga kamar gwamma ta mutu.

 Mu Shaidun Jehobah ne kuma ’yan ikilisiyarmu suna taimaka mana sosai! Alal misali, akwai ranar da wata yarinya daidai tsarana ta aika mana katin gaisuwa kuma a ciki ta gaya mana yadda take kaunarmu kuma ta ce tana shirye ta taimaka mana. Samun irin wannan abokiyar yana da ban karfafa!

 Littafi Mai Tsarki ma ya taimaka mini sosai. Alal misali, daya daga cikin nassosin da nake jin dadin karantawa sosai shi ne, Zabura 34:18, wadda ta ce Ubangiji yana kusa da wadanda suka karaya. Wani kuma shi ne, Ibraniyawa 13:6, da ta ce: “Ubangiji shi ne mataimakina, ba zan ji tsoro ba.”

 Nassin nan na biyu yana karfafa ni sosai. Abin da ya fi tsorata ni shi ne sanin cewa wata rana mahaifiyata za ta mutu. Ina kaunarta sosai kuma ina jin dadin kasancewa tare da ita. Wannan nassin ya taimake ni in kasance da gaba gadi cewa zan iya jimre duk abin da zai faru a nan gaba.

 Wani abin tsoro kuma shi ne, ana iya gadān cutar EDS. Mahaifiyata ta gadā wannan cutar daga wurin mahaifiyarta ne, yanzu ni kuma na gadā daga wajen mahaifiyata. Amma Ibraniyawa 13:6 ta ce, Jehobah zai zama “mataimakina” idan ina fama.

 A yanzu, ina gode wa Allah a duk yanayin da na tsinci kaina, kuma ba na gwada yanayina na yanzu da na dā ko kuma yawan damuwa da abin da zai faru a nan gaba. Nakan yi bakin ciki sosai idan na soma tunani a kan abubuwan da mahaifiyata take iya yi a dā da yadda take yanzu. Littafi Mai Tsarki ya ce yanayin da muke fuskanta na “lokaci kadan” ne amma a nan gaba za mu ji dadin irin rayuwa da babu rashin lafiya har abada.—2 Korintiyawa 4:17; Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.

 Ka yi tunani a kan wannan: Me ya taimaka wa Emmaline ta kasance da karfin zuciya? Ta yaya za ka kasance da karfin zuciya idan kana fuskantar yanayi mai wuya?

 Labarin Emily

 A lokacin da nake makarantar sakandare ne mahaifina ya soma fama da ciwon bakin ciki. Sai yana min kamar wani mutum ne dabam nake gani, ba mahaifina ba. Tun daga lokacin da mahaifina ya kamu da wannan cutar, yakan yi bakin ciki ba kadan ba, ya razana ba gaira ba dalili kuma yana yawan damuwa. Ya yi fama da wannan yanayin har tsawon shekaru 15 yanzu. Hakika, na san cewa ba ya jin dadi sam da yadda yake bakin ciki, don ya san cewa bai kamata ya yi bakin ciki ba!

 Mu Shaidun Jehobah ne kuma ’yan ikilisiyarmu suna taimaka mana sosai. Suna da kirki sosai kuma sun fahimci irin yanayin da mahaifina yake ciki, saboda haka ba sa sa shi ji kamar bai da amfani a cikin ikilisiyar. Yadda mahaifina yake jimrewa da wannan yanayin ya sa na dada kaunarsa.

 Idan na yi tunanin yadda mahaifina yake da fara’a da kuma koshin lafiya a dā, ganin yadda yake fama da wannan mummunan yanayin a yanzu yana sa ni bakin ciki sosai.

 Duk da haka, mahaifina yana iya kokarinsa ya kasance da ra’ayi mai kyau. Akwai lokacin da yanayinsa ya yi muni sosai kuma domin haka, ya kudurta zai karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, ko da ayoyi kadan ne kawai. Hakan ya taimaka masa sosai. Wannan kokarin da ya yi ya sa na yi alfahari da shi sosai.

 Ina son nassin da ke Nehemiya 8:10 (Littafi Mai Tsarki), inda aka ce: “Farin cikin da Ubangiji ya ba ku shi ne karfinku.” Idan na je taro kuma na shagala da ayyukan ibada a wurin, farin cikin da nake samu a wurin yana taimaka mini in kawar da bakin ciki daga zuciyata. Hakan yana taimaka mini in yini lafiya. Abin da yake faruwa da mahaifina ya koya mini cewa Jehobah zai iya taimakonmu ko da wane irin yanayi ne muke fuskanta.

 Ka yi tunani a kan wannan: Ta yaya Emily ta taimaki mahaifinta a lokacin da yake rashin lafiya? Ta yaya za ka iya taimaka ma wanda yake fama da ciwon bakin ciki?