Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Za Ka Iya Koyo da Kyau Idan Ba Ka Cikin Makaranta?

Za Ka Iya Koyo da Kyau Idan Ba Ka Cikin Makaranta?

 Dalibai da yawa a yau suna halartan makaranta a gida. Idan haka kake yi, me za ka yi don ka amfana sosai? Ga wasu shawarwari. *

 Shawarwari biyar da za su taimaka maka ka yi nasara

 •   Ka tsara ayyukanka. Ka tsara ayyukanka kamar yadda za ka yi da a ce kana wurin makaranta. Ka kebe lokacin yin abubuwa kamar ayyukan makaranta, da aikace-aikace a gida da dai sauran abubuwa masu muhimmanci. Za ka iya canja tsarin idan da bukata.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “A yi kome . . . a shirye.”​—⁠1 Korintiyawa 14:⁠40.

   Wata mai suna Katie ta ce: “Ka tsara abubuwa da za ka yi a kowace rana kamar kana makaranta. Ka yi abubuwan da ya kamata ka yi a lokacin da ya kamata ka yi su.”

   Ka yi tunani a kan wannan: Me ya sa yake da kyau ka rubuta tsarin da ka yi kuma ka ajiye shi a wurin da zai yi maka saukin gani?

 •   Kana bukatar ka kame kanka. Idan kana so ka nuna cewa ka manyanta, wajibi ne ka yi abin da ya kamata ka yi ko da ba ji yin hakan ba. Kada ka rika jan kafa!

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ku taba zama da rashin kwazo.”​—⁠Romawa 12:⁠11.

   Wata mai suna Alexandra ta ce: “Kame kai yana da wuya sosai. Yana da sauki mutum ya nemi hujjar da za ta sa shi ya ce, ‘Zan yi aikin makaranta an jima.’ Amma idan lokacin yin aikin ya zo, sai ya sake fasawa, a karshe kuma sai aiki ya yi masa yawa.”

   Ka yi tunani a kan wannan: Ta yaya yin ayyukan makaranta a wuri daya a kowane lokaci zai taimaka maka ka kasance da kamun kai?

 •   Ka zabi wurin da za ka rika yin nazari. Ka tabbata cewa kana da dukan abubuwan da kake bukata don nazari. Ka tsara wurin da za ka yi nazarin da kyau, amma kada ka tsara shi yadda zai sa ka soma jin barci yayin da kake nazari. Wurin aiki ne ba wurin barci ba ne! Idan ba ka da wurin da ka tsara don yin ayyukan makaranta, watakila a lokacin da kake son ka yi ayyukan makaranta, ka je daki ka yi hakan .

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Shirye-shirye na mai ƙwazo lallai sukan kai ga yalwata.”​—⁠Karin Magana 21:⁠5.

   Wata mai suna Elizabeth ta ce: “Ka cire kwallo da wasan bidiyo da jitarka daga inda za ka rika ganin su kuma ka saita wayarka yadda ba za ta yi kara ba. Idan kana so ka yi nazari da kyau, kana bukatar wurin da babu abubuwan da za su janye hankalinka.”

   Ka yi tunani a kan wannan: Wadanne canje-canje ne za ka iya yi a wurin da kake nazari don ka samu ka tattara hankalinka a wuri daya?

 •   Ka koyi yadda za ka rika mai da hankali ga abin da kake yi. Ka mai da hankali ga abu guda da kake yi, kuma kada ka yi kokarin yin abubuwa da yawa a lokaci daya. Idan ka yi kokarin yin abubuwa da yawa a lokaci daya, za ka iya yin kuskure kuma zai iya daukanka dogon lokaci kafin ka kammala aikin.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku yi amfani da kowane zarafi” da kyau.​—⁠Afisawa 5:⁠16.

   Wata mai suna Olivia ta ce: “Tattara hankalina wuri daya yana yi mini wuya idan wayata tana kusa da ni. Nakan bata lokaci sosai ina yin abubuwa marasa amfani.”

   Ka yi tunani a kan wannan: Za ka iya kara yawan lokaci da kake kokari ka mai da hankali ga yin wani abu?

 •   Ka rika daukan hutu. Ka fita yawo ko ka dan tuka keke ko kuma ka motsa jiki. Yin wani abu da kake jin dadin yi zai iya sa ka wartsake. Amma wani littafi mai suna School Power ya ce, “Ka kammala aikinka kafin nan.” Ya kara cewa: “Za ka ji dadin hutunka sosai bayan ka riga ka gama abubuwan da ya kamata ka yi.”

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku dan huta.”​—⁠Markus 6:31.

   Wata mai suna Taylor ta ce: “A makaranta za ka iya koyan yin amfani da kayan kade-kade ko kuma ka koyi zane-zane. Ban gane amfani wadannan abubuwan ba sai da na soma zuwa makaranta a gida. Kari ga karatun da kake yi, kana bukatar ka koyi yin wasu abubuwa.”

   Ka yi tunani a kan wannan: Wane irin hutu ne zai taimaka maka ka sami karfin yin ayyukan makaranta?

^ Akwai hanyoyi da yawa na halartan makaranta daga gida. Ka yi amfani da shawarwarin da aka tattauna a wannan talifin da suka dace da yanayinka.