Abin da kake bukata: Yadda za ka yi magana da ladabi

Iya magana abu ne mai muhimmanci da zai

  • sa wasu su fahimce ka.

  • sa ka san abin ya sa ba a yarda ka yi abin da kake so ba.

Hakika, idan kana son a bi da kai a matsayin wanda ya manyanta, zai dace ka san yadda za ka yi magana da ladabi. Ta yaya za ka iya yin haka?

Ka kame kanka. Magana da ladabi tana bukatar kamun kai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wawa ya kan furta dukan fushinsa; Amma mai-hikima ya kan danne shi ya kwaɓe shi.Misalai 29:11.

Me ake nufi? Ka guji yin guna guni, yin zugum, rufe kofa da karfi, ko kuma kaiwa da kawowa a cikin gida. Irin halin nan zai sa a janye wasu gata da aka ba ka a dā—maimakon karin ’yanci.

Ka yi kokari ka fahimci ra’ayin iyayenka. Misali: A ce iyayenka ba sa son ka je wani liyafa. Maimakon ka yi gardama da su, kana iya tambaya:

“Idan na je da wani amini da ya manyanta fa?”

Kila har ila iyayenka ba za su yarda ba. Amma idan ka fahimci dalilinsu, kila za ka iya yin wata shawara dabam da za su amince.

Bin dokokin iyayenka kamar biyan bashin banki ne—idan ka ci gaba da biya, za a dada yarda da kai

Ka yi abin da zai sa iyayenka su yarda da kai. Alal misali, wani da banki ke binsa bashin kudi. Idan yana biyan kudin kadan kadan, lallai zai sa bankin ya amince da shi har ma su sake ba shi bashi nan gaba.

Haka ma yake cikin iyali. Biyayya ga iyayenka kamar bashi ne. Idan ba ka biya, wato idan ba ka yi musu biyayya ba, ba za su yarda da kai ba.”

Amma, idan ka nuna dogararka—ko a kananan batu—iyayenka za su iya gaskata da kai.